Uba Sani: Tinubu Ya Fi Kowane Shugaban Najeriya Kawo Ci Gaba a Arewa
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi fatali da hasashen cewa Arewa ba za ta goyi bayan Bola Tinubu a zaɓen 2027 ba, yana mai cewa zai samu ƙuri'u fiye da na 2023
- Gwamnan ya bayyana haka ne bayan ikirarinsa a kan irin taimakon da ya ce shugaban ya yi wa Arewacin Najeriya ta fuskar kawo ayyukan ci gaba da gina jama'a
- Yana wannan martani ne bayan hasashen da ke yawo cewa Tinubu zai rasa goyon bayan mutanen da ke Arewa duba da halin da ake zargin gwamnati ta tsoma su a ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da ayyukan ci gaba a Arewacin Najeriya fiye da duk wani shugaba da ya gabace shi.
Uba Sani ya ce hakan na bayyana ne ta hanyar manyan ayyukan more rayuwa, tallafin noma da kuma inganta harkokin lafiya da gwamnatin Tinubu ta aiwatar a yankin.

Source: Twitter
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise News a ranar Talata, 30 ga watan Yuni, 2026.
Uba Sani ya yabi aikin Tinubu
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa Gwamna Uba Sani ya yi amannnar cewa jama'ar Arewa za su saka wa Bola Tinubu da kuri'a saboda aikin alherinsa.
A kalamansa:
"Duk abin da nake faɗa ina jingina shi ne da bayanai da ƙididdiga. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Arewacin Najeriya abin da babu wani shugaba da ya taɓa yi."
Ya ƙara da cewa:
"Ina tabbatar maka babu wani shugaban ƙasa da ya kawo wa Arewa irin wannan ci gaba cikin shekaru ukun da suka gabata kamar yadda Bola Ahmed Tinubu ya yi. Ina magana ne bisa bayanai da ƙididdiga."
Arewa za ta zabi Tinubu - Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa jama'a za su yi wa Tinubu ruwan kuri'a sama da abin da ya samu a zaben 2023 saboda alherinsa.

Source: Twitter
A cewarsa:
"Ni ne gwamnan jihar Kaduna, kuma ina tabbatar maka Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai samu ƙuri'a fiye da waɗanda ya samu a zaɓen 2023."
Uba Sani ya danganta wannan hasashe da irin manyan ayyukan da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a Kaduna da sauran jihohin Arewa.
Ya ce aikin titin Abuja zuwa Kaduna, wanda ya daɗe yana tangal-tangal, na gab da kammala bayan gwamnatin Tinubu ta biya sama da Naira biliyan 600 daga cikin kuɗin kwangilar da ta kai kusan Naira biliyan 750.
Game da titin Kaduna zuwa Birnin Gwari, gwamnan ya ce gwamnatin Tinubu ta fara sakin kuɗin aikin da ya kai Naira biliyan 178, bayan an yi watsi da titin sama da shekaru 25.
Ya kara da cewa akwai sauran manyan ayyuka da gwamnatin Tinubu ta yi, wanda Arewa ta amfana sosai ta fuskoki da dama.
Uba Sani ya magantu kan Tinubu
A baya, kun samu labarin cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi hasashen kuri'un da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai samu a jiharsa a 2027 yayin da kakar zaben ke gabato wa.
Sanata Uba Sani ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai samu kuri'u masu kyau a Kaduna saboda ayyukan da ya aiwatar, wanda zai jawo jama'a su saka masa da alherin a rumfunan zaben.
Gwamnan ya bayyana cewa shugaban kasar da jam'iyyar APC ba su da wata adawa a jihar Kaduna saboda jama'a na goyon bayansu tare da bayyana yakinin cewa Tinubu zai koma kujerarsa a shekara mai zuwa.
Asali: Legit.ng


