Rigimar Rarara da Takwaransa ta Munana, an Shiga Zagin Juna a Dandalin Twitter

Rigimar Rarara da Takwaransa ta Munana, an Shiga Zagin Juna a Dandalin Twitter

  • An yi cacar baki mai zafi tsakanin shahararrun mawakan Najeriya guda biyu watau Dauda Kahutu Rarara da David Adeleke wanda aka fi sani da Davido
  • Rigimar ta fara ne bayan Rarara ya soki Davido kan yadda ya dauki matsalar rashin tsaron Najeriya ya kai ta wajen gasar cin kofin duniya
  • Mawakan biyi sun yi ta musayar yawu a tsakaninsu inda har lamari ya kai ga sun zazzagi juna a shafukan sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - An samu barkewar cacar baki tsakanin shahararrun mawaka a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara da David Adeleke wanda aka fi sani da Davido.

Cacar bakin ta barke ne tsakanin mawaki Rarara da Davido kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Najeriya.

Rarara ya yi rigima da mawaki Davido
Shahararrun mawaka, Dauda Kahutu Rarara da Davido Hoto: Dauda Kahutu Rarara, Davido
Source: Facebook

Legit Hausa ta lura cewa shahararrun mawakan biyu sun yi musayar yawu ne a shafukansu na X a ranar Laraba, 17 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

'Zabe ne a gabansa': Yan majalisa sun dura kan Tinubu game da tsaron ƙasa

Dalilin rigimar Rarara da Davido

Rigimar ta fara ne bayan Rarara ya nuna takaicinsa kan yadda Davido ya kai matsalar tsaron Najeriya a wajen bikin kofin duniya a Amurka.

Mawakin na APC ya nuna cewa bai dace Davido ya nuna sunayen dalibai da malaman da aka sace a jihat Oyo ba, a wajen gasar.

Rarara ya bayyana cewa abin da Davido ya yi tamkar kunyata Najeriya ne maimakon tallafawa kasar wajen magance rashin tsaro.

Cacar baki ta barke tsakanin Rarara da Davido

Bayan fitar da bidiyon da Rarara ya yi, mawaki Davido ya tanka masa, inda ya nuna takaici a shafinsa na X kan yadda bai iya fadin sunansa da kyau ba.

Ya nuna Rarara na kiran sunansa da Debidoo maimakon Davido, wanda hakan ke nuna bai ma iya fadin sunan ba.

Daga nan Rarara ya tanka a shafinsa na X, inda gargadi Davido kan ya shiga taitayinsa.

Kara karanta wannan

Ran Rarara ya baci da aka soki Tinubu kan tsaro, ya zargi Davido da bata Najeriya

"Kashiga taitayinka"

Davido ya sake yi martani kan kalaman Rarara, inda ya nuna cewa bai da lokacinsa saboda mawakin ba shi da ilmi kuma sakarai ne.

Lamarin ya kai ga zage-zage

Davido ya rubuta a shafinsa na X cewa:

"Da ace kana da ilimi da na tsaya nayi magana dakai. Amma komai baka sani ba, sakarai kawai."
"Da farko, duk wanda yake da kishin Najeriya ba zai yi shiru kan matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasa ba, kuma ba zai hana wasu bayyana damuwarsu a kai ba."
"Rashin tausayi da fifita son rai ko zama karen 'yan siyasa, da fifita son rai fiye da muradun al’umma ba abin alfahari ba ne."
"Ka kasance mai kishin ƙasarka, ka daina fifita siyasa a kan gaskiya, sannan ka ji tsoron Allah a cikin duk abin da kake yi."
Davido da Rarara sun zazzagi juna
Mawaka a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara da Davido Hoto: Dauda Kahutu Rarara, Davido
Source: Facebook

Rarara ya sake yin martani ga Davido a shafinsa na X, inda ya kira shi da dakiki tare da gaya masa cewa ya jira martanin da zai yi masa.

Kara karanta wannan

Jarumin fim ya maka INEC, hadimin Wike a kotu, ya buƙaci diyyar N10bn

"Dakiki ka jira martani na"

Daga karshe mawakin na APC ya bayyana cewa duk wanda yake jin haushinsa ta ya je ya rungumi tiransifoma kawai.

Ya rubuta a shafinsa na X cewa:

"Duk wanda ya kejin haushina yaje ya rungumi transformer"

An watsawa Rarara kudi a wajen taro

A wani labarin kuma, kun ji cewa an ja kunnen wata mata bayan ta watsa kudi ga shahararren mawaki, Dauda Kahutu Rarara a wajen taro.

Matar sanye da kayan APC ta watsawa Rarara kudin yayin da yake yin wakarsa ta 'Omo Logo' domin karrama shugaban kasa Bola Tinubu a wajen taron.

Sai dai, an gargade ta kan wannan dabi’a, domin dokokin Najeriya sun haramta watsa kudi ko amfani da su ta hanyar da ke bata darajarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng