Tinubu, Ribadu da Ministan Sun Sha Yabo daga Kiristoci, Sun Tabo Maganar Trump
- Ƙungiyar matasan Kiristocin Arewacin Najeriya ta yabawa Bola Tinubu, Nuhu Ribadu da Janar Christopher Musa
- Ta ce yabon da Donald Trump ya yi wa Najeriya ya nuna ƙoƙarin gwamnati wajen kare rayuka, musamman al'ummomin Kiristoci da ke Arewacin ƙasar
- NNCYA ta buƙaci 'yan Najeriya su haɗa kai wajen tallafa wa matakan samar da zaman lafiya, tare da ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa kan tsaro da musayar bayanan sirri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ƙungiyar Northern Nigeria Christian Youth Association (NNCYA) ta yabawa salon mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ƙungiyar ta kuma yabawa Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa kan yaki da ta'addanci.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da Sakataren ƙungiyar na ƙasa, Bason Sunday, ya fitar, cewar Tribune.
Kungiyar ta ce yabon da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Najeriya kan yaƙi da ta'addanci da kare al'ummomin Kirista ya tabbatar da ƙoƙarin da suke yi.
Ƙungiyar ta ce wannan yabo daga fannin diflomasiyya ya nuna irin jajircewar gwamnatin tarayya wajen yaƙi da rashin tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al'umma, musamman a Arewacin Najeriya.
NNCYA ta ce amincewar da Trump ya nuna ga nasarorin tsaron Najeriya wata babbar shaida ce cewa gwamnatin Tinubu tana aiki tuƙuru wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar.
Ƙungiyar ta kuma yabawa jagorancin Mallam Nuhu Ribadu, tana mai bayyana shi a matsayin wanda ya tsara ingantaccen haɗin bayanan sirri, ya rungumi warware rikice-rikice cikin hikima, tare da farfaɗo da tsarin tsaron Najeriya.
Sunday ya ce ƙungiyar ta yi maraba da yabon da Trump ya yi kan Taswirar Haɗin Gwiwar Tsaro tsakanin Amurka da Najeriya ta 2026, da tura dakarun musamman na Amurka domin tallafa wa sojojin Najeriya, da kuma nasarar haɗin gwiwar yaƙi da ta'addanci, ciki har da rahoton kashe manyan shugabannin ISIS a yankin Tafkin Chadi.
Ya ce:
"Muna yaba wa Mallam Nuhu Ribadu saboda jagorancinsa wajen tsara bayanan sirri, warware rikice-rikice cikin hikima da kuma jagorantar Kwamitin Haɗin Gwiwa na Amurka da Najeriya. Ƙoƙarinsa ya farfaɗo da tsarin tsaron Najeriya, ya tarwatsa hanyoyin 'yan ta'adda tare da dawo da amincewar jama'a ga hukumomin tsaro."
Ya ƙara da cewa waɗannan nasarori na duniya da kuma waɗanda aka samu a fagen daga ba za su yiwu ba face saboda kyakkyawan tsari da ƙwarewar shugabannin tsaron Najeriya.
Ƙungiyar ta kuma yabawa Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), bisa abin da ta bayyana a matsayin jajircewa, adalci da shugabanci mai samar da sakamako wajen jagorantar rundunar sojin ƙasa.
Sunday ya ƙara da cewa:
"Muna matuƙar yaba wa Ministan Tsaro saboda jajircewarsa, shugabanci mai haɗa kowa da kuma mayar da hankali kan sakamako.
A matsayinsa na jagoran da ya fahimci yanayin tsaron Arewacin Najeriya, ƙudirinsa na kare dukkan al'umma da dawo da zaman lafiya a yankunan da rikici ya shafa abin yabawa ne."
Matashin ya yaba wa ministan tsaro
Mun ba ku labarin cewa wasu na ci gaba da caccakar masu yada maganar murabus din ministan tsaro, Christopher Musa a mukaminsa.
Wani masoyin Bola Tinubu, Khamis Musa Darazo ya bukaci 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki su daina siyasantar da batun tsaro.
Darazo ya yabawa Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, saboda jajircewa wajen yaki da ta'addanci.
Asali: Legit.ng


