Zaben 2027: Pantami Ya Sake Samun Tagomashi a Takarar Gwamnan Jihar Gombe
- Tsohon mai neman takarar gwamnan Gombe a karkashin PDP, Mohammed Manu Malala, ya goyi bayan Prof. Isa Ali Ibrahim Pantami
- Mohammed Manu Malala ya ce ya ajiye burinsa na neman takarar gwamna ne domin hadin kan jam’iyya da ci gaban Gombe
- Ya kuma musanta rahotannin cewa ya kai kara kan zaben fitar da gwani na dan takarar PDP na gwamna a kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Tsohon mai neman takarar gwamnan Gombe a karkashin jam’iyyar PDP, Mohammed Manu Malala, ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar jam’iyyar, Prof. Isa Ali Ibrahim Pantami, gabanin zaben gwamnan jihar na 2027.
Malala, wanda tsohon babban sakatare ne a jihar Gombe, ya bayyana goyon bayansa ne a cikin wata sanarwa da kungiyar yada labarai ta PDP a jihar ta fitar.

Source: Facebook
Abba Sani Pantami ya sanya sanarwar a ranar Litinin, 20 ga watan Yulin 2026 a shafinsa na Facebook
Ya ce ya dauki wannan matakin ne bayan Pantami ya zama dan takarar jam’iyyar daya tilo da ya tsallake tantancewar da hedikwatar PDP ta kasa ta gudanar, sannan reshen jam’iyyar na jihar Gombe ya tabbatar da takararsa.
Malala ya ajiye burinsa na takara
A cewar Malala, ya yanke shawarar ajiye burinsa na neman takarar gwamna ne domin tabbatar da hadin kan jam’iyya da kuma ci gaban jihar Gombe baki daya.
Ya kuma musanta rahotannin da ke cewa ya kalubalanci tsarin zaben dan takarar gwamnan PDP a kotu, inda ya dage cewa bai kai karar jam’iyyar ba, kuma ba shi da niyyar yin hakan.
Malala ya bayyana cewa Pantami shi kadai ne daga cikin masu neman takarar da ya samu nasarar tsallake tantancewar PDP, sannan hedikwatar jam’iyyar ta kasa ta ba shi takardar shaidar tsallake tantancewa.
“Saboda haka, ya zama dan takara daya tilo da aka tabbatar da cancantarsa, sannan aka tabbatar da shi ba tare da hamayya ba."
“Bisa wannan tsari, babu wani dalili na doka da zai bai wa duk wani mai neman takara da bai yi nasara ba ko wanda bai tsallake tantancewar ba damar kalubalantar sakamakon a kotu,” in ji shi.
Ya bukaci hadin kan PDP
Tsohon mai neman takarar ya bukaci dukkan mambobin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki da ke da sha’awar ci gaban Gombe da su hada kai wajen goyon bayan Pantami, wanda ya bayyana a matsayin shugaba mai hangen nesa da ke da damar sauya jihar.
Ya kuma yi kira ga sauran masu neman takarar gwamnan PDP da su hada kai da dan takarar jam’iyyar domin karfafa damar PDP na lashe zaben gwamnan jihar na 2027.

Source: Facebook
Pantami ya yi godiya
Da yake mayar da martani, Pantami ya gode wa Malala bisa goyon bayan da ya ba shi da kuma amincewar da ya nuna ga shugabancinsa.
Dan takarar gwamnan na PDP ya tabbatar masa da cewa gwamnatinsa za ta kasance mai tafiya kowa, inda ya yi alkawarin yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin moriyar jam’iyyar da al’ummar jihar Gombe baki daya..

Kara karanta wannan
Takarar Sheikh Pantami a jihar Gombe ta samu gagarumin goyon baya gabanin zaben 2027
Batun karar Farfesa Pantami
A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Gombe ta kammala sauraron ƙarar da mai neman takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Khamisu Mailantarki, ya shigar gabanta.
Khamisu Mailantarki ya shigar da karar ne yana ƙalubalantar sahihancin zaɓen fitar da gwamnan da jam'iyyar ta gudanar a ranar 26 ga Mayu, 2026.
Asali: Legit.ng

