Tafiyar Pantami Ta Kara Karfi a Gombe, Mutanen Sanata Bayero Nafada Sun Tsaya a PDP

Tafiyar Pantami Ta Kara Karfi a Gombe, Mutanen Sanata Bayero Nafada Sun Tsaya a PDP

  • Jagorori da mambobin tsarin siyasar tsohon mataimakin shugaban majalisa, Sanata Bayero Nafada, sun bayyana goyon bayansu ga Sheikh Isa Ali Pantami
  • 'Yan siyasar daga ƙananan hukumomi 11 na jihar Gombe sun ce ba za su bi Bayero Nafada zuwa jam'iyyar APC ba duk da ficewarsa daga PDP
  • Yayin wata ganawa a Gombe, tawagar ta sha alwashin yin aiki tukuru domin tabbatar da nasarar Pantami a zaɓen gwamnan Gombe na shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gombe – Jagorori da mambobin tsarin siyasar tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai, Usman Bayero Nafada, daga dukkan ƙananan hukumomi 11 na Gombe sun goyi bayan ɗan takarar gwamna na PDP, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami.

Matakin ya biyo bayan ficewar Sanata Bayero Nafada daga jam'iyyar PDP zuwa APC, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a harkokin siyasar jihar.

Kara karanta wannan

Sanata na hannun daman Kwankwaso ya sa labule da shugaban APC da Barau

Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami da mutanen Bayero Nafada. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Pantami ya wallafa a Facebook cewa tawagar ta samu jagorancin shugaban tafiyar siyasar Bayero Nafada na jiha, Hon. Malachi Karfe Kanadi, tare da Hon. Umaru Bajam Bayero da sauran fitattun jagorori daga ƙananan hukumomi 11.

Maganar mutanen Bayero Nafada

Da yake jawabi a madadin tawagar, jagororin sun bayyana cewa duk da kasancewarsu masu biyayya ga Sanata Bayero Nafada tsawon shekaru, ba za su bi shi zuwa jam'iyyar APC ba.

Sun jaddada cewa biyayyarsu tana nan daram ga jam'iyyar PDP, tare da bayyana cikakken goyon bayansu ga takarar Sheikh Isa Ali Pantami.

A cewarsu, za su yi aiki ba dare ba rana domin tabbatar da nasarar Pantami da PDP a zaɓen gwamnan Jihar Gombe na shekarar 2027.

Martanin Sheikh Isa Ali Pantami

Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya karɓi tawagar tare da wasu manyan jiga-jigan PDP da suka haɗa da Hon. Jalo Ahmed Ganga.

Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da tsohon shugaban asibitin koyarwa na tarayya da ke Gombe, Dr. Abubakar Saidu Yagi, Hon. Usman Gurama da kuma Hon. Ahmed Abubakar Walama (Sarkin Malaman Gombe).

Kara karanta wannan

Takarar Sheikh Pantami a jihar Gombe ta samu gagarumin goyon baya gabanin zaben 2027

Sheikh Isa Ali Pantami
Lokacin da Sheikh Sheikh Isa Ali Pantami ke magana a taron. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Pantami ya gode wa tawagar bisa amincewa da goyon bayan da suka nuna masa, yana mai tabbatar masu da cewa za a riƙa tafiya tare da su a dukkan matakan siyasar da ke gaba.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa haɗin kai da jajircewa za su taimaka wajen bai wa PDP nasara a zaɓen gwamnan jihar a shekarar 2027 da yardar Allah.

Ficewar Bayero Nafada daga PDP

Lamarin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan tsohon Sanatan da ya wakilci Gombe ta Arewa kuma tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai, Usman Bayero Nafada, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.

A cikin wasiƙar murabus ɗinsa mai ɗauke da kwanan watan 12 ga Yuli, 2026, Ledership ta wallafa cewa Nafada ya danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida da kuma matsalolin shugabanci da suka daɗe suna addabar PDP.

Inuwa Yahaya ya kafa kwamitin sulhu na APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da kwamitin sulhu na jam'iyyar APC mai mambobi 25.

Kara karanta wannan

Bauchi: Tsohon kwamishina ya zama mataimakin dan takarar gwamna a APC

An ɗaura wa kwamitin alhakin sasanta rikice-rikicen cikin gida, ƙarfafa haɗin kai da kuma shirya jam'iyyar domin samun gagarumar nasara a zaɓen shekarar 2027.

Yayin ƙaddamar da kwamitin a gidan gwamnati da ke Gombe, ya bayyana cewa APC na da burin nasara dukkan kujerun jihar tare da samar wa Bola Tinubu ƙuri'u miliyan 1 a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng