Yadda masoya suka yi dafifi a yayin yakin neman zaben Buhari a Benuwe

Yadda masoya suka yi dafifi a yayin yakin neman zaben Buhari a Benuwe

Abin ba’a cewa komai sai san barka, dubun dubatan al’ummar jahar Benuwe da suka hada da magoya bayan jam’iyyar APC, da kuma masoya shugaban kasa Muhammadu Buhari ne suka tarbi shugaban a yayin gangamin yakin neman zabensa a garin Makurdi.

Legit.ng ya ruwaito a ranar Laraba, 6 ga watan Feburairu ne shugaba Buhari ya isa garin Makurdi, babban birnin jahar Benuwe, domin halartar yakin neman zabensa a karo na biyu daya gudana a filin wasa na Aper Aku.

Yadda masoya suka yi dafifi a yayin yakin neman zaben Buhari a Benuwe
Buhari a Benuwe
Asali: Facebook

KU KARANTA: Zamu halaka duk wanda yayi mana katsalandan a zabe – El-Rufai ga yan kasashen waje

Tun da misalin karfe 9 na safe ne magoya baya suka fara taruwa a filin wasan, haka zalika yansanda masu bada hannu akan titi sun yi aiki tukuru don ganin sun magance matsalar cunkoson ababen hawa a yayin ziyarar ta Buhari.

A dalilin cincirindon mutanen da suka halarci wannan gangami na Buhari, ta kai ga motocin haya na Bus suna daukan fasinjo a cikin sashin daukan kaya, yayin da baburan haya da aka fi sani da suna Achaba suka dinga haukan har mutane uku akan babur guda.

Yadda masoya suka yi dafifi a yayin yakin neman zaben Buhari a Benuwe
Buhari a Benuwe
Asali: Twitter

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta zanta da wani jagoran kungiyar goyon bayan Buhari mai taken, Benuwe Alliane for Good Governance, BAGG, Dakta Aondokaa Asambe, wanda ya jinjina ma Buhari bisa kokarin da yayi na dawo da martabar kasar a idon duniya.

Asambe ya bayyana cewa jajircewar da Buhari ya nuna tun bayan darewarsa kujerar shugaban kasa a shekarar 2015 abu ne wanda ba’a taba samunsa ba a Najeriya, din haka yayi kira da jama’an Benuwe dasu zabi Buhari a zaben 16 ga watan Feburairu na 2019.

Yadda masoya suka yi dafifi a yayin yakin neman zaben Buhari a Benuwe
Buhari a Benuwe
Asali: Facebook

Shima a jawabinsa, tsohon kaakakin majalisar dokokin jahar Benuwe, Stepehn Tsav ya danganta tururuwan da jama’an Benuwe suka yi zuwa gangamin da irin soyayyar da suke yi ma Buhari, tare da amincewa da manufofinsa.

Daga karshe ya tabbatar ma shugaban kasa Buhari da cewa al’ummar Benuwe ba zasu bashi kunya a ranar 16 ga wata ba, amma yayi kira ga Buhari daya kara dagewa wajen farfado da komadar tattalin arzikin kasar nan.

Yadda masoya suka yi dafifi a yayin yakin neman zaben Buhari a Benuwe
Buhari a Benuwe
Asali: Facebook

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel