'Mun Daina Bautawa Siyasa', Fahad Dankabo Ya Kawo Sabon Salo a Siyasar Kano

'Mun Daina Bautawa Siyasa', Fahad Dankabo Ya Kawo Sabon Salo a Siyasar Kano

  • Fahad Muhammad Dankabo ya ce lokaci ya yi da siyasa za ta fara yi wa al'umma hidima maimakon al'umma su rika bautar siyasa a Najeriya
  • Tsohon mai neman kujerar majalisar wakilai ya bukaci matasa su mara wa shugabanni masu yi wa jama'a hidima baya a zaben 2027 cikin lumana
  • Dankabo ya bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugabannin da ya kamata a sake bai wa dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Kano - Tsohon mai neman kujerar majalisar wakilai a mazabar Kabo/Gwarzo, Fahad Muhammad Dankabo, ya bukaci matasan Najeriya su rungumi sabon salo a siyasar 2027.

Fahad Dankabo ya ce lokaci ya yi da siyasa za ta fara yi wa al'umma hidima maimakon al'umma su rika bautar siyasa.

Fahad Dankabo ya nemi matasa su dauki sabon salon siyasa a Kano.
Fahad Muhammad Dankabo yana magana ga magoya bayansa a Kano. Hoto: Fahad Muhammad Dankabo
Source: Facebook

Dankabo ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kamar yadda Legit Hausa ta gani a ranar Litinin, 20 ga Yulin 2026.

Kara karanta wannan

'Na shirya a yi tonon silili': Pantami ya bugi kirji kan abubuwan alheri da ya yi

"Mun daina bautawa siyasa" - Dankabo

Tsohon mai neman takarar ya ce wannan ne sabon akidar siyasar da yake son ganin ta fara daga karamar hukumar Kabo zuwa Gwarzo, tare da fatan za ta bazu zuwa sauran sassan kasar.

A cewarsa, tsofaffin 'yan siyasa da magabata sun yi kokari sosai wajen gudanar da gwagwarmayar siyasa, yana mai jaddada cewa ya kamata a ci gaba da girmama gudunmawar da suka bayar.

"Allah ya jikan wanda suka gabata. Wanda suke da rai, Allah ya kara musu lafiya da kwanciyar hankali. Wadanda suke kan mulki kuma, Allah ya kama muku yasa ku gama lafiya."

- Fahad Dankabo.

Sai dai ya ce lokaci ya yi da za a sauya tunanin cewa dole ne mutane su bautar wa siyasa kafin su samu ci gaba daga wadanda ke mulki.

Kira ga matasa kan zaben 2027

Fahad Dankabo ya kuma bukaci matasa su gudanar da harkokin siyasar 2027 cikin lumana da hakuri, yana mai cewa nasara tana hannun Allah.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya hango abin da zai hana Tinubu cin zaɓe, ya ba shi mafita

Ya ce wajibi ne matasa su hada kai wajen tallafa wa shugabannin da yake kira "masu yi wa al'umma hidima," domin samun ci gaba mai dorewa.

A cewarsa:

"Allah ya yi mana, amma fa 'yan uwana matasa sai mu daure rakuman mu, sai mu tsarkake niyoyin mu, mu yi tawakkali—Allah zai ji mana da komai da kowa, musamman shaidanun cikin al’umma."
Fahad Dankabo ya ce ya kamata a sake ba Tinubu da Abba Yusuf dama a 2027.
Fahad Muhammad Dankabo, tsohon dan takarar majalisar wakilai a Kano. Hoto: Fahad Muhammad Dankabo
Source: Facebook

Wadanda Dankabo ke goya wa baya a 2027

A cikin sakonsa, Dankabo ya bayyana cewa yana goyon bayan Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin zaben shekarar 2027.

Ya ce a fahimtarsa ta siyasa, Tinubu shi ne mafi dacewa cikin wadanda ake sa ran za su nemi shugabancin kasa a zaben mai zuwa.

Sai dai ya bukaci mutane kada su bari sabanin ra'ayi ya hana su hada kai wajen neman shugabanni da za su fifita muradun jama'a.

"Allah ya kai mu 2027 da rai da lafiya a Farke (ba a Mafarki ba kuma ba’a barzaku ba Insha Allah). Allah yajikan mu ba dan mun mutu ba."

Kara karanta wannan

Matasa 9 sun rasu a hanyar neman arziki daga Sokoto zuwa Legas

- Fahad Dankabo.

Jagoran matasan Kwankwasiyya ya koma APC

A wani labari, mun ruwaito cewa, Fahad Dankabo ya yi maraba da Sadeeq Garo bayan sauya shekarsa zuwa APC, yana mai bayyana cewa matasa irinsa ne Kano ke bukata.

Dankabo ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta mayar da Kano cibiyar kasuwanci, tattalin arziki da al'adu a Najeriya da Afrika ta Yamma.

A wata sanarwar da ya fitar, Sadeeq Garo ya bayyana babban dalilin da ya sanya bar jam'iyyar NDC ta su Sanata Rabiu Kwankwaso zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com