"Muna da Dan Takara"; Gwamna Ya Sutale Takwaransa kan Batun Goyon Bayan Tazarcen Tinubu a 2027

"Muna da Dan Takara"; Gwamna Ya Sutale Takwaransa kan Batun Goyon Bayan Tazarcen Tinubu a 2027

  • Alex Otti na jihar Abia ya ce Hope Uzodimma ba zai iya magana a madadin dukkan gwamnonin Kudu maso Gabas ba
  • Gwamnan Imo ya ce dukkan gwamnonin Kudu maso Gabas sun amince su goyi bayan takarar Bola Tinubu a wa’adi na biyu
  • Alex Otti ya ce jam’iyyarsa ta Labour Party za ta goyi bayan dan takararta a zaben shugaban kasa mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Umuahia, Abia – Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya mayar wa takwaransa na Imo, Hope Uzodimma, martani kan kalamansa dangane da goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Tinubu.

Gwmana Otti ya yi martanin ne bayan Uzodinma ya ce dukkan gwamnonin jihohin Kudu maso Gabas biyar sun amince su goyi bayan yunkurin Shugaba Bola Tinubu na sake tsayawa takara a wa’adi na biyu.

Otti ya yi wa Uzodinma martani
Gwamna Alex Otti na jihar Abia da Hope Uzodinma Hoto: Alex C Otti, Hope Uzodimma
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta ce Gwamna Otti ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Yulin 2026 yayin taron manema labarai na watan Yuli da ya gudanar a Umuahia.

Kara karanta wannan

ADC ta gamu da koma baya, na kusa da El Rufai ya fice daga jam'iyyar a Kaduna

Bai magana da bakin kowa

Da yake martani kan kalaman gwamnan Imo, Otti ya ce Uzodimma na da damar bayyana ra’ayinsa a matsayinsa na gwamna da kuma mutum, amma bai kamata ya yi magana a madadin dukkan gwamnonin Kudu maso Gabas ba.

“Kun ce gwamnan jihar Imo ya fadi wani abu game da sake zaben shugaban kasa. Ban tabbata na ji hakan ba. Amma idan ya fadi hakan, hakkinsa ne ya fada a matsayinsa na gwamna da kuma mutum. Amma ba zai iya magana a madadin kowa ba."
“Na tabbata idan lokacin ya yi, mutane za su yanke shawara. Ina ganin har yanzu lokaci ya yi.”

- Gwamna Alex Otti

Otti na goyon bayan manufofin Tinubu

Sai dai Otti ya sake jaddada goyon bayansa na tsawon lokaci ga wasu manufofin tattalin arzikin gwamnatin tarayya, ciki har da cire tallafin man fetur, yana mai cewa matsayinsa kan batun ya samo asali ne tun kafin a zabe shi gwamna.

Kara karanta wannan

Fashola: Tsohon gwamna ya fadi dalilin kin sukar gwamnatin Tinubu

“Shin ina adawa da shugaban kasa ya sake tsayawa takara a wa’adi na biyu? Babu ko kadan. Jama’a ne za su yanke shawara."
“Yana da damar tsayawa takara a wa’adi na biyu. Haka kuma sauran wadanda suke son tsayawa takara suna da damar yin hakan. A karshe, akwatin zabe ne, kai da ni, za mu yanke shawarar abin da zai faru.”

- Gwamna Alex Otti

Otti na da dan takara a zaben 2027
Gwamna Alex Otti na jihar Abia Hoto: @alexottiofr
Source: Twitter

Wane dan takara Otti zai goyi baya?

Gwamnan na Labour Party ya kara da cewa, duk da cewa jam’iyyarsa za ta goyi bayan dan takararta na shugaban kasa a zabe mai zuwa, ba za ta hana kowa amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba shi na tsayawa takara ba.

“Jam’iyyata ita ce Labour Party kuma tana da nata dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa. Matukar muna da ‘yan takara, za mu goyi bayansu. Amma hakan ba yana nufin za mu je mu yi fada da kowa ba,” in ji shi.

Otti ya musanta komawa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Abia, Dr. Alex Otti, ya yi magana kan rade-radin cewa ya fice daga jam'iyyar LP.

Gwamna Alex Otti ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa cewa ya bar jam’iyyar LP ya koma APC mai mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng