Gwamnatin Zamfara Ta Fara Daukar Sababbin Ma'aikata, Matasa 3050 Za Su Samu Aiki
- Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da cewa ta bude kofar ɗaukar malamai 3,050 domin cike giɓin malamai a makarantun gwamnati
- Daga cikin ka'idojin da aka shimfida; dole ne masu neman aikin su kasance 'yan asalin Zamfara masu shekaru tsakanin 18 zuwa 35
- Za a ba masu koyar da darussa masu muhimmanci kamar Turanci, Lissafi da Kimiyya fifiko yayin da za a rufe neman aikin ranar 16 ga Yulin 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta fara aikin ɗaukar sababbin malamai 3,050 domin koyarwa a makarantun firamare da ƙananan makarantun sakandare na gwamnati.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Zamfara za ta dauki ma'aikatan ne a wani yunƙuri na magance ƙarancin malamai da inganta harkar ilimi a jihar.

Source: Facebook
An buɗe shafin neman aiki a Zamfara
Kwamitin ɗaukar malaman ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma'aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta jihar, Maryam Yahaya Shantali, ta sanya wa hannu, in ji rahoton Punch.
Sanarwar ta ce an buɗe shafin neman aikin ta yanar gizo ga ƙwararrun 'yan asalin jihar Zamfara da suka cika ka'idojin da aka gindaya.
A cewar kwamitin, manufar ɗaukar malaman ita ce ƙarfafa ilimin bai ɗaya ta hanyar tura ƙwararrun malamai zuwa makarantun da ke karkara da sauran wuraren da ake fama da ƙarancin malamai.
An buɗe shafin neman aikin tun ranar 2 ga Yulin 2026, kuma za a rufe shi a ranar 16 ga Yuli, inda aka gargaɗi cewa ba za a karɓi buƙatun da suka wuce wa'adin ba.
Sharuddan neman aikin
Kwamitin ya bayyana cewa dole masu neman aikin su kasance 'yan asalin jihar Zamfara, masu shekaru tsakanin 18 zuwa 35.
Haka kuma, dole ne su mallaki ɗaya daga cikin takardun shaidar koyarwa da suka haɗa da NCE, B.Ed., B.Sc. (Ed.), B.A. (Ed.), ko kuma B.Sc./B.A. tare da PGDE.
Baya ga haka, ana buƙatar masu neman aikin su mallaki takardar shaidar TRCN ko shaidar yin rajista, takardar kammala bautar ƙasa (NYSC), tare da amincewa cewa za a iya tura su aiki zuwa kowace unguwa ko ƙauye a jihar.
Takardun da ake buƙata
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa masu neman aikin za su loda dukkan takardun da ake buƙata, ciki har da shaidun karatu, takardar shaidar asalin jihar, takardar haihuwa ko rantsuwar bayyana shekaru, ingantaccen katin shaida da hoton fasfo.
Kwamitin ya ce za a bai wa malamai masu ƙwarewa a darussa masu muhimmanci fifiko, kamar Turanci, Lissafi, Kimiyya da Fasaha, Kimiyyar Noma, Kwamfuta, Nazarin Al'umma, Ilimin Jiki da Lafiya.
Sauran darussan da za a ba fifiko sun haɗa da Tarihin Najeriya, Al'adu da Fasahar Ƙirƙira, Ilimin Gida, Larabci, Ilimin Yara Ƙanana (ECCDE), Nazarin Ilimin Firamare (PES), Addinin Musulunci da Harshen Hausa.

Source: Getty Images
Za a yi CBT bayan tantancewa
Kwamitin ya kuma umarci masu neman aikin su biya kuɗin neman aiki na Naira 1,000, wanda ba za a mayar ba, ta hanyar dandalin Pay Zamfara da aka haɗa da shafin neman aikin.
Sanarwar ta ce waɗanda suka yi nasarar tantancewar farko ta yanar gizo ne kawai za a gayyata domin rubuta jarabawar kwamfuta (CBT).
A ƙarshe, kwamitin ya ce wannan shiri na nuna ƙudirin Gwamna Dauda Lawal na inganta ilimin bai ɗaya a jihar ta hanyar ɗaukar ƙwararrun malamai.
An gano ma'aikatan bogi a Zamfara
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa an gano kura-kurai a tsarin daukar ma'aikatan da ke aiki da gwamnatin jihar Zamfara.
Wannan ya biyo bayan rahoton kwamitin da gwamna Dauda Lawal Dare ya kafa domin tsefe ma'aikata kafin biyan mafi karancin albashi.
Gwamnan ya ce an gano wasu ma'aikatan bogi, da kananan yara da wadanda ya dace a ce sun yi ritaya kuma su na karbar albashi.
Asali: Legit.ng


