'An Gama Komai': Ƴan Arewa Sun Tabbatar wa Tinubu Nasara a Zaɓen 2027
- Ƙungiyar North Central Agenda (NCA) ta fadi yadda za ta taimaka wurin tabbatar da nasarar Bola Tinubu a 2027
- Ta bayyana goyon bayanta ga sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027, tana mai cewa nasararsa a yankin ta zama tabbaci
- Kungiyar ta ce gwamnatin Tinubu ta kawo manyan ayyukan tituna, ilimi, noma da tsaro, lamarin da ya inganta rayuwar al'ummar Arewa ta Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ƙungiyar North Central Agenda (NCA) ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Ƙungiyar ta jaddada cewa za ta ba da gudummawa domin ya sake neman wa'adi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Source: Twitter
Shugaban ƙungiyar, Ene Ogbole, ta bayyana hakan ne yayin wani taron kwana guda da aka gudanar a Abuja, cewar TheCable.
Tabbacin da ƙungiya ta ba Tinubu
Ogbole ya ce tattaunawa na ci gaba a yankin Arewa ta Tsakiya ƙarƙashin manufar Renewed Hope ta gwamnatin Tinubu.
Ƙungiyar ta ce nasarar shugaban a yankin Arewa ta Tsakiya ta riga ta zama abin da ba za a iya sauyawa ba.
Ogbole ta kuma yi watsi da sabon cece-kuce kan tikitin Musulmi da Musulmi na jam'iyyar APC, tana mai cewa 'yan Najeriya sun riga sun yanke hukunci a kan batun tun lokacin babban zaɓen shekarar 2023.
Ta ce kafin gwamnatin Tinubu ta hau mulki a watan Mayun 2023, yankin Arewa ta Tsakiya ya dade yana fama da ƙarancin manyan ayyukan raya ƙasa da kuma matsalolin tsaro.
A cewarta, manufofin gwamnatin sun samar da sabon fata ta hanyar saka hannun jari a manyan tituna, noma, ilimi da tsaro, wanda ya haifar da ci gaba mai anfani ga yankin.
Ta lissafa manyan ayyuka kamar hanyar Calabar–Ebonyi–Benue–Kogi–Nasarawa–Abuja, hanyar Sokoto–Badagry, hanyar Akwanga–Jos–Bauchi–Gombe–Maiduguri, hanyar Suleja–Minna da kuma aikin faɗaɗa hanyar Lokoja–Okene a matsayin muhimman ayyukan da ke amfani yankin.

Source: Facebook
Ayyukan alheri da Tinubu ya yi
A cewarta, yadda gwamnatin Bola Tinubu ta raba ayyukan raya ƙasa cikin adalci a dukkan shiyyoyin Najeriya ya sauya yanayin yankin daga rashin kulawa zuwa ci gaban tattalin arziki da manyan ayyukan more rayuwa.
Saboda haka, ta ce ƙungiyar za ta tattara gagarumin goyon baya a dukkan jihohin Arewa ta Tsakiya shida da Babban Birnin Tarayya domin tabbatar da sake zaɓen Tinubu a shekarar 2027.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, wanda Babatunde Benard ya wakilta, ya ce sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke yi suna shimfiɗa tubalin bunƙasar Najeriya na dogon lokaci.
Ya ce shugaban yana ɗaukar matakai masu wahala amma masu muhimmanci domin gyara tattalin arzikin ƙasa, duk da cewa sakamakonsu ba zai bayyana nan take ba.
Gwamna ya fadi tasirin Tinubu kan sauran takwarorinsa
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce Shugaba Bola Tinubu ya fi sauran masu neman takarar shugaban ƙasa.
Abdullahi Sule ya ce banbancin da ke tsakanin Tinubu da abokan hamayyarsa ya yi kama da dare da rana.
Gwamnan ya bayyana ayyukan raya ƙasa, ilimi da ci gaban kasuwar hannayen jari a matsayin nasarorin gwamnatin Tinubu.
Asali: Legit.ng

