"Ya Fi Su": Gwamna Sule Ya Fadi Fannin da Tinubu Ya Yi Wa Atiku, Obi Fintinkau

"Ya Fi Su": Gwamna Sule Ya Fadi Fannin da Tinubu Ya Yi Wa Atiku, Obi Fintinkau

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce Shugaba Bola Tinubu ya fi sauran masu neman takarar shugaban ƙasa
  • Abdullahi Sule ya ce banbancin da ke tsakanin Tinubu da abokan hamayyarsa ya yi kama da dare da rana
  • Gwamnan ya bayyana ayyukan raya ƙasa, ilimi da ci gaban kasuwar hannayen jari a matsayin nasarorin gwamnatin Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya kare ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na sake tsayawa takara.

Gwamna Sule ya ce tarihin aikinsa ya fi na sauran masu neman shugabancin ƙasa a zaɓen 2027 nesa ba kusa ba.

Gwamna Sule ya yabi Shugaba Bola Tinubu
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da Shugaba Bola Tinubu Hoto: Abdullahi A Sule Mandate, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Gwamna Sule ya bayyana haka ne a shirin Politics Today na Channels Television ranar Talata, 21 ga watan Yulin 2026.

Meye bambancin Tinubu da 'yan adawa?

Gwamnan ya ce banbancin da ke tsakanin Tinubu da abokan hamayyarsa ya yi kama da “dare da rana”, yana mai nuni da abin da ya kira ƙwarewar shugaban ƙasa, jarumtaka da hangen nesa cikin shekaru uku da suka gabata.

Kara karanta wannan

Masoyan Tinubu sun mayar wa Kwankwaso martani kan tikitin Musulmi Musulmi

Ya yi wannan bayani ne yayin da yake amsa tambayar dalilin da ya sa ya kamata ’yan Najeriya su goyi bayan tikitin Tinubu da Shettima maimakon yiwuwar haɗin gwiwar ’yan adawa, ciki har da tikitin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ko Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi.

“Dare da rana ne. Ba za ka iya kwatanta su ba ko kaɗan. Idan ka duba tarihin wannan shugaban ƙasa, idan ka duba jarumtakarsa, idan ka duba irin aikinsa, idan ka duba hangen nesansa, idan ka duba abin da ya faru cikin shekaru uku da suka gabata, babu ɗaya daga cikin mutanen da ka ambata da bai taɓa riƙe wani matsayi ba.”
“Yanzu ka ɗauki wannan tarihin ka gwada shi da tarihin da na faɗa maka yanzu cikin shekaru uku da suka gabata. Dare da rana ne. Ba za ka iya kwatanta su ba.”

- Gwamna Abdullahi Sule

Sule ya fayyace dalilin zaɓen Tinubu

Da aka ƙara matsa masa ya bayyana takamaiman dalilan da ya sa ya kamata ’yan Najeriya su zaɓi Tinubu, gwamnan ya sake jaddada cewa nasarorin da shugaban ya samu a mulki sun bambanta shi da sauran masu neman takara.

“Na gaya maka, aiki, jarumtaka da hangen nesan wannan shugaban ƙasa,” in ji shi.

Kara karanta wannan

"Ya mutu yana kaina"; Sababbin bayanai sun fito kan mutuwar Janar Abacha

Sule ya ce duk da cewa masu sukar gwamnati kan yi nuni da rashin tsaro a matsayin babbar matsala a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, matsalar ta daɗe kafin gwamnatin yanzu kuma an samu ci gaba mai auna a kanta.

“Na san abin da za ka fito da shi, rashin tsaro, sai ka ce kamar rashin tsaro ya fara ne cikin shekaru uku da suka gabata."
“Amma idan ka duba aikinsa, har ma a fannin rashin tsaro, kuma na yi farin ciki da na zauna a nan lokacin da kuke tattaunawa da Janar Musa, domin Janar Musa ya gaya muku cewa ko a fannin tsaro ma, an samu babban ci gaba.” In ji shi
Gwamna Sule ya yabawa Tinubu
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa Hoto: Abdullahi A Sule Mandate
Source: Facebook

Gwamna ya jero nasarorin Tinubu

Gwamnan ya kuma yi nuni da ayyukan raya ababen more rayuwa, sauye-sauyen ilimi da alamomin ci gaban tattalin arziƙi a matsayin hujjojin nasarorin gwamnatin.

A cewarsa, girman ayyukan more rayuwa da ake gudanarwa a faɗin ƙasar ba a taɓa yin irinsu ba a baya.

Gwamna Sule ya nada sabon sarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya nada sabon Sarkin Udege da ke karamar hukumar Nasarawa (Osu Ajiri na Udege).

Gwamna Sule ya nada Alhaji Suleiman Ahmed-Eko a matsayin sabon Osu Ajiri na masarautar Udege da ke ƙaramar hukumar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng