Gwamna Sule Ya Nada Sabon Sarki Mai Martaba a Najeriya, An Fara Tura Sakon Taya Murna
- Alhaji Suleiman Ahmed-Eko ya samu nasarar zama sabon Osu Ajiri na Udege, Sarki mai daraja ta daya a al’ummar Afo ta jihar Nasarawa
- Gwamnatin jihar Nasarawa ce ta tabbatar da nadin sabon Sarkin a wata sanarwa da ta fitar yau Laraba, 15 ga watan Afrilun 2026
- An haifi Ahmed Eko a ranar 2 ga watan Yuni, 1972, kuma ya kammala karatu a Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Nasarawa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Nasarawa, Nigeria - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya amince da nadin sabon Sarkin Udege da ke karamar hukumar Nasarawa (Osu Ajiri na Udege).
Gwamna Sule ya nada Alhaji Suleiman Ahmed-Eko a matsayin sabon Osu Ajiri na masarautar Udege da ke ƙaramar hukumar Nasarawa, kuma matakin zai fara aiki nan take.

Source: Facebook
Gwamna Sule ya nada Sarkin Udege
Jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito cewa gwamnatin Nasarawa ta sanar da wannan nadi ne ta hannun kwamishinar kananan hukumomi, harkokin masarautu da ci gaban al'umma, Alhaja Amina Mu’azu-Maifata.
Kwamishinar ta sanar da nadin basaraken a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, 15 ga watan Afrilun 2026 a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa da ke Arewa ta Tsakiya.
Ta ce naɗin ya fara aiki nan take, inda ta taya sabon sarkin murna tare da yi masa fatan samun nasara a mulkinsa.
Yadda aka zabi Suleiman Ahmed-Eko
Gwamnatin Nasarawa ta bayyana cewa an zaɓi Ahmed-Eko ne bayan tattaunawa da shawarwari da Majalisar Sarakunan gargajiya ta jihar, inda aka cimma matsaya.
An haifi Suleiman Ahmed-Eko, wanda a yanzu ya zama sarki mai daraja ta ɗaya a al’ummar Afo, ranar 2 ga watan Yuni, 1972, kuma ya kammala karatu a Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Nasarawa.
Sabon sarkin ya gaji marigayi Alhaji Halilu Bala-Usman, tsohon mataimakin gwamnan tsohuwar Jihar Filato, wanda ya rasu a ranar 25 ga watan Mayu, 2025.
Har ila yau, kwamishinar ta bayyana cewa Alhaji Suleiman Ahmed-Eko yana da iyali, mata da kuma ‘ya’ya, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.

Source: Facebook
An fara taya sabon sarkin murna
Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK), ƙarƙashin jagorancin Barista Nuhu Egya, ta miƙa saƙon taya murna ga Mai Martaba Alhaji Suleiman Ahmed Eko bisa naɗinsa a matsayin sabon Osu Ajiri na Udege.
Ƙungiyar ta bayyana cewa zaɓe da tabbatar da Ahmed Eko a matsayin sarki mai daraja ta ɗaya na ƙabilar Afo wata shaida ce ta gudunmawar da ya bayar ga ƙasa musamman a fannin kasuwanci da jajircewarsa wajen bunƙasa al’umma.
Gwamna Bala ya rabawa sarakuna motoci
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya raba daruruwan motoci na aiki ga sarakunan gargajiya.
Motocin da aka raba wa sarakunan sun hada da sababbin saloon na GMC 14, bas-bas na Toyota, motocin daukar kaya na Hilux, da kuma fiye da motoci 100 kirar Toyota Camry.
Gwamna Bala ya bayyana cewa rabon motocin wani bangare ne na kokarin gwamnatinsa na karfafa shugabanci a matakin kasa da kuma bunkasa hulda da al’umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

