Dan Sanda Ya Yi Murabus a Bauchi, Ya Ce Shekaru 2 Bai Samu Albashinsa ba
- Rundunar ’yan sandan Bauchi ta fara bincike kan murabus ɗin wani ɗan sanda da ya ce bai samu damar cire albashinsa ba tsawon shekaru biyu
- Rundunar ta ce binciken farko ya nuna an riƙa biyan albashin jami’in akai-akai, amma matsalar BVN ce ta hana shi samun kuɗinsa
- ’Yan sanda sun ce jami’in ya karya dokar amfani da kafafen sada zumunta bayan ya bayyana ƙorafinsa da murabus ɗinsa a intanet
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Rundunar ’yan sandan Bauchi ta fara bincike kan lamarin wani jami’i da ya sanar da murabus, yana zargin hana shi samun albashinsa shekaru biyu.
Jami’in mai lamba F/No. 524180, CPL Yusuf Aliyu, ya bayyana murabus ɗinsa daga rundunar ’yan sandan Najeriya ta kafafen sada zumunta.

Source: Facebook
Kakakin rundunar ’yan sandan Bauchi, SP Nafi’u Habib ya bayyana haka a Facebook inda ya ce rundunar ta san da wata wasiƙa da ake cewa jami’in ne ya rubuta.
Zargin da dan sanda ke yi a Bauchi
Dan sandan ya yi ikirarin cewa tsawon wannan lokaci bai samu damar cire albashin da ake biya masa ba, lamarin da ya sa ya bayyana damuwarsa.
Habib ya ce wasiƙar ta bazu a kafafen yaɗa labarai daban-daban, inda jami’in ya bayyana dalilin da ya sa ya ɗauki matakin murabus.
Ya ce kwamishinan ’yan sanda, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan yadda aka takaita asusun bankin jami’in.
A cewar kakakin, binciken farko ya nuna hukumomin ’yan sanda sun riƙa biyan albashin jami’in a kan lokaci ba tare da tsaiko ba.
Sai dai ya bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga rashin daidaito a bayanan Bank Verification Number, wato BVN, na jami’in.
Ya ce sunan da ke haɗe da BVN ɗin jami’in ya sha bamban gaba ɗaya da sunan da ke kan asusun da ake tura albashinsa.

Kara karanta wannan
Daliban ABU Zaria sun kera na'urar da makafi za su rika tafiya da ita cikin salama
Wannan rashin daidaito, a cewar rundunar, ne ya sa aka takaita asusun bankin, abin da ya hana jami’in cire albashin da aka biya masa.
Habib ya ce:
“Binciken farko ya nuna cewa hukumomin ’yan sanda sun riƙa biyan albashin jami’in cikin lokaci kuma ba tare da tsaiko ba.”
Ya ƙara da cewa matsalar da aka samu ta samo asali ne daga bambancin bayanan BVN da sunan da ke kan asusun albashin jami’in.
Rundunar ta kuma nuna damuwa kan yadda jami’in ya zaɓi amfani da kafafen sada zumunta wajen bayyana ƙorafinsa da sanar da murabus ɗinsa.
Ta ce ya kamata jami’in ya bi hanyoyin cikin gida da rundunar ta tanada domin gabatar da ƙorafi da neman a warware matsalarsa.
Ta'addanci: An cafke mutane 2 a Bauchi
Mun ba ku labarin cewa rundunar 'yan sandan Bauchi ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da ba 'yan bindiga bayanan sirri domin satar mutane a Alkaleri.
Ana zargin matasan sun taimaka wajen harin da aka kai wani mutum mai shekara 46, wanda ya samu raunin harbin bindiga yayin ƙoƙarin tserewa.
Kwamishinan 'yan sanda ya tabbatar da an miƙa shari'ar zuwa sashen binciken manyan laifuka tare da kira ga jama'a su ci gaba da ba da sahihan bayanai.
Asali: Legit.ng
