Yan Kabilar Igbo a Arewa Sun Nuna Kwarin Guiwa, Za Su ba Tinubu Kuri’u Miliyan 2

Yan Kabilar Igbo a Arewa Sun Nuna Kwarin Guiwa, Za Su ba Tinubu Kuri’u Miliyan 2

  • Shugaban ƙungiyar siyasar kabilar Igbo a jihohin Arewa 19 da Abuja sun yi Shugaba Bola Tinubu alkawarin ƙuri’u
  • John Amaechi Onwe ya ce ’yan kabilar Igbo mazauna Arewa sun yanke shawarar shiga siyasar yankin, maimakon zaman ’yan adawa
  • Ya ce ƙungiyar ta kafa babbar hanyar tuntuɓar jama’a daga jihohi zuwa ƙananan hukumomi da ƙungiyoyin gari domin tallafa wa APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - ’Yan kabilar Igbo mazauna jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja sun yanke shawarar marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.

Sun kuma bayyana aniyarsu ta tallafa wa jam’iyyar APC tare da ƙudirin samar wa shugaban ƙasa aƙalla ƙuri’u miliyan biyu.

Igbo da ke Arewa za su sama wa Tinubu miliyoyin kuri'u
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu yana jawabi a taro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Darakta-Janar na 'Igbo Political Movement, 19 Northern States and FCT', Cif John Amaechi Onwe, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Miyetti Allah ta kaɗa hantar Tinubu, ta fada masa sharaɗin sake zaɓensa a 2027

Igbo a Arewa sun gaji da adawa

Onwe ya ce matakin ya biyo bayan shawarar al’ummar Igbo na shiga siyasar Arewa sosai, maimakon ci gaba da kasancewa a matsayin ’yan adawa.

Ya ce ƙungiyar ta samar da babbar hanyar haɗa kai da jama’a, wadda ta ƙunshi shugabannin al’ummar Igbo a jihohin Arewa 19 da Abuja.

Onwe ya ƙara da cewa tsarin ya haɗa da shugabannin matakin jiha, shugabannin ƙananan hukumomi da kuma ƙungiyoyin ’yan asalin garuruwa.

A cewarsa, za a yi amfani da wannan tsari wajen wayar da kan jama’a da tattara goyon baya ga APC a lokacin zaɓen 2027.

Tinubu ya kara samu goyon baya a Arewa
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya a wurin taron APC. Hoto: All Progressives Congress.
Source: Twitter

Yawan Igob da ke zaune a Arewa

Ya bayyana cewa ’yan Ibo da ke zaune a Arewa suna da yawan masu kada ƙuri’a, don haka jam’iyyun siyasa da ’yan takara ba za su iya yin watsi da su ba.

Ya ce:

“Za mu bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ƙuri’u da ba za su gaza miliyan biyu ba. Na ce ba za su gaza miliyan biyu ba, wannan shi ne mafi ƙarancin burinmu."

Kara karanta wannan

An bukaci Tinubu ya hakura da shiga takara a zaben 2027

Shugaban ya ce tsarin zai taimaka wajen kai saƙonnin siyasa ga masu zaɓe a matakin jiha, ƙananan hukumomi, ƙungiyoyin gari da kuma mazabu, cewar Punch.

Onwe, wanda ya ce akwai kusan ’yan Igbo miliyan 15 a Arewacin Najeriya da Abuja, ya ce ƙuri’unsu za su taka muhimmiyar rawa a zaɓen 2027.

Ya ƙara da cewa al’ummar Igbo ta yanke shawarar daina gudanar da siyasar adawa, tare da goyon bayan gwamnatin da ke kan mulki.

“Mu, ’yan kabilar Igbo da muke zaune a Arewacin Najeriya, ba ma shirye mu ci gaba da kasancewa ’yan adawa ba. Mun yi hakan a baya, amma bai amfane mu ba. Don haka, gaba ɗaya, mun amince mu goyi bayan gwamnatin da ke mulki, tun daga matakin ƙasa har zuwa jihohi.”

- Cewar Onwe

Za a roki Obi ya janye wa Tinubu

A baya, an ji cewa kungiyar Renewed Hope for Greater Nigeria ta ce ta shirya wata ganawa a Kudu maso Gabas domin nema wa Bola Tinubu sauki a 2027.

Shugaban kungiyar a yankin ya ce za su nemi Emeka Anyaoku da Ebitu Ukiwe su jagoranci tawaga zuwa wajen Obi.

Ya ce janyewar Obi ba zai kawo ƙarshen burinsa na shugabancin Najeriya ba, sai dai dagewa zuwa lokacin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.