Fadar Shugaban Ƙasa: 'Tinubu Ya Fitar da Mara 'Da Kunya, Ya Kamata a Saka Masa a 2027'

Fadar Shugaban Ƙasa: 'Tinubu Ya Fitar da Mara 'Da Kunya, Ya Kamata a Saka Masa a 2027'

  • Fadar shugaban kasa ta yi magana game da neman sake zaben shugaba Bola Tinubu a babban zaben 2027 da ke tafe ganin irin ayyukan da ya yi wa kasa
  • Ta ce idan aka yi duba na tsanaki, za a gano dalilai masu karfi da za su tabbatar da nasarar shugaban da ke neman wa'adi na biyu a zabe mai zuwa
  • Daga cikin abubuwan da aka y alfahari da su har da batun inganta tsaro a lokacin da jama'a, musamman a Arewa ke kuka da garkuwa da mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Fadar shugaban kasa ta ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da mulki yadda ya kamata, kuma hakan ya sa ya cancanci sake neman wa'adi na biyu a zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Ganduje ya fadi abin da zai hana Obi da Atiku buge Tinubu a 2027

Babban mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da ayyuka na musamman, Tunde Rahman, ya bayyana haka yayin da ya jagoranci duba ayyukan gwamnatin tarayya da ta jihar Kogi a yankin Kogi ta Yamma.

Fadar shugaban kasa ta yi maka kan sake zaben Tinubu
Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Nigerian Tribune ta wallafa cewa Rahman ya ce tawagar ta ga yadda gwamnati ta aiwatar da ayyuka a bangaren kiwon lafiya da hanyoyi a wasu kananan hukumomin jihar.

Gwamnatin Tinubu ta yi aiki a Kogi

A cewarsa, an sanar da su cewa jihar Kogi na da kananan hukumomi 21, kuma matakin farko na aikin gyaran hanyoyi ya shafi guda takwas.

Ya ce:

"Mun gani da idanunmu yadda gwamnati ta zuba jari a bangaren kula da lafiyar iyalai da kuma gina hanyoyi a wasu kananan hukumomi."

Rahman ya kuma yabawa gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo, yana mai cewa halayensa na tawali'u da adalci sun bayyana a irin ayyukan da gwamnatin jihar ke aiwatarwa.

Tinubu ya cancanci wa'adi na 2 - Fadar Shugaban kasa

Rahman ya kara da cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun bai wa jihohi karin kudaden da suke amfani da su wajen gudanar da ayyukan raya kasa.

Kara karanta wannan

Kashin 'yan bindiga ya bushe, gwamnati ta ɓullo da dabarun yaƙi da ta'addanci a Najeriya

Fadar shugaban kasa ta ta bayyana ayyukan da ta yi a Kogi
Taswirar jihar Kogi Arewa ta Tsakiya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya ce gwamnatin jihar ta saka fasaha cikin tsarin tsaron makarantu domin kare dalibai da malamai.

Ya bayyana cewa ana amfani da na'urorin sa ido da ke hade da cibiyar kula da tsaro da ke Lokoja, tare da hadin gwiwar 'yan sanda, mafarauta da jami'an tsaron sa-kai da aka horas.

Ya ce:

"Ina ganin shugaban kasa ya yi abin da ya isa ya cancanci wa'adi na biyu, kuma nasarorin da ya samu ne za su yi masa magana tare da ba shi damar sake lashe zabe a 2027."

Yan takara sun amsa kiran Tinubu

A baya, mun wallafa cewa wasu daga cikin wadanda su ke neman takarar gwamna a jam'iyyar APC reshen jihar su na ci gaba da nuna rashin jin dadinsu a kan zaben fitar da gwani.

Duk da cewa an kafa kwamitin sulhu a jam'iyyar, kuma har ya fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin sasanta rikicin, da alama lamarin ya girmama da har za a kai gaban shugaban kasa.

Sai dai masu neman takarar sun ce za su ci gaba da zama a jam'iyyar APC duk da rashin jin dadinsu kan zaben yayin da shugaban kasa Bola Tinubu ya kira su a zauna domin a yi sulhu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng