"Yana Son Raba Najeriya"; Sheriff Ya Soki Obi kan Neman Tinubu Ya Yi Murabus
- A cikin 'yan kwanakin nan, Peter Obi, ya rika fitowa yana neman shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus daga mukaminsa
- Tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, wanda jigo ne a APC ya fito ya yi martani ga dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar NDC a zaben 2027
- Ali Modu Sheriff ya bayyana cewa Peter Obi shi ne mutum mafi rashin cancanta da zai fito ya nemi Shugaba Tinubu ya yi murabus
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ali Modu Sheriff, tsohon gwamnan Jihar Borno, ya yi zargin cewa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, ya yi amanna da kasar Biyafara.
Ali Modu Sheriff ya kuma yi zargin cewa Peter Obi yana fafutukar raba Najeriya ne ta hanyar burinsa na zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan
Segalink ya yi maganar da ka iya zama barazana ga takarar Peter Obi da Kwankwaso a 2027

Source: Facebook
Ali Modu Sheriff ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 6 ga watan Yulin 2026 yayin wata tattaunawa a shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake mayar da martani kan kiran da Obi ya yi kwanan nan na cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus ko ya janye neman tazarce saboda tabarbarewar tsaro a kasar.
Me Ali Modu Sheriff ya ce kan Peter Obi?
Ali Modu Sheriff ya yi ikirarin cewa, idan aka yi la'akari da abin da Obi ya yi amanna da shi, shi ne "mutumin da ya fi kowa rashin cancanta" da zai yi irin wannan bukata.
Ya yi zargin cewa tsohon gwamnan bai taba yin tir da ayyukan haramtacciyar kungiyar fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB) ba, ko kuma akidar kungiyar da kudurorinta.
“Wannan kasa, Najeriya, ta yi yakin basasa. Shugabanninmu sun sadaukar da rayukansu domin yin wannan yakin don ganin kasar ta zauna a hade, shugabanni daga arewa da na kudu baki daya."
“Dalilin yakin shi ne bukatar ballewa da Ojukwu ya yi. Peter Obi, har zuwa wannan lokaci, yana fafutukar raba Najeriya ne."
“Ta yaya? Domin ya yi amanna da Biyafara. Bai taba yin tir da Biyafara ba. Bai taba yin tir da IPOB ba."
“Biyafara ballewa ce. Shugabanninmu sun yi yaki domin ganin kasar ta zauna a hade. Shi kuma yana son ya raba Najeriya.”
- Ali Modu Sheriff
Ali Modu Sheriff ya kalubalanci Peter Obi
Yayin da aka tambaye shi ta yaya mutumin da yake neman zama shugaban kasan Najeriya zai so ya raba kasar, Ali Modu Sheriff ya kalubalanci Obi da ya fito fili ya karyata wannan zargi.
“Ya kamata ya karyata hakan. Kamata ya yi ya zo wannan gidan talabijin ya ce shi bai yi amanna da raba kasar nan ba.”
- Ali Modu Sheriff

Source: Facebook
Peter Obi ya bukaci Tinubu ya yi murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Pter Obi, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi murabuas daga mukaminsa.
Peter Obi ya bukaci Tinubu ya yi murabus ne saboda bayanan da IMF ta fitar masu nuna cewa an kashe kudaden Najeriya a boye.
A cewarsa, kudaden da aka ruwaito an kashe din, wadanda ya kiyasta sun kai kusan Naira tiriliyan 8.83, an kashe su ne a wajen tsarin kasafin kudin da aka amince da shi.
Asali: Legit.ng

