A Karshe, Peter Obi Ya Bar Boye Boye, Ya Fadi dalilin Daukar Kwankwaso Mataimakinsa
- Peter Obi ya ce ya fadi dalilin zabar Sanata Rabiu Kwankwaso a matsayin abokin takararsa a zaben shekarar 2027
- Obi ya musanta jita-jitar sabani tsakaninsa da Kwankwaso, yana mai cewa suna aiki tare domin samar da sauyin da zai inganta rayuwar 'yan Najeriya
- Dan takarar NDC ya ce haɗa magoya bayan Obidient da Kwankwasiyya ba zai haifar da rikici ba, domin burinsu ɗaya ne na ceto Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC mai adawa a Najeriya, Peter Obi, ya yi karin haske kan dalilin daukar Rabiu Kwankwaso.
Peter Obi ya bayyana cewa ya zaɓi Rabiu Kwankwaso, a matsayin abokin takararsa na zaɓen 2027 saboda suna da manufa iri ɗaya ta yaƙi da talauci ta hanyar ilimi da bunƙasa tattalin arziki.

Source: Facebook
Musabbabin alakar Obi da Kwankwaso
A wata hira da jaridar The Sun ta wallafa, Obi ya ce haɗin gwiwarsu ya samo asali ne daga ƙimomi iri ɗaya da kuma hangen nesa na sake gina Najeriya.
Ya jaddada cewa su biyun sun fi mayar da hankali kan kawo sauyi mai amfani fiye da siyasar anfani ta kashin kai.
Tsohon gwamnan Anambra ya ce Kwankwaso ya daɗe yana ba ilimi da bunƙasa jarin ɗan Adam muhimmanci, kuma hakan ya yi daidai da shirinsa na farfaɗo da Najeriya.
Obi ya ce:
"Kwankwaso yana da falsafar fitar da mutane daga talauci. Ni ma haka nake. Ya yi imani da ilimi, domin ba za a sauya al'umma ba tare da ilimi ba."
Ya ƙara da cewa ilimi ne zai kasance ginshiƙin manufofinsa, domin shi ne hanyar sauya al'umma da gina jarin ɗan Adam da Najeriya ke buƙata domin ci gaba.

Source: UGC
Obi ya yi karin haske kan 'sabani' da Kwankwaso
Obi ya kuma musanta rahotannin da ke cewa akwai saɓani tsakaninsa da Sanata Rabiu Kwankwaso.
Ya ce bai san dalilin da ya sa ake yaɗa irin waɗannan jita-jita ba, domin ba a taɓa ganin su suna rikici ba.
A cewarsa, matsalolin siyasa na samo asali ne daga shugabanci mai anfani ta kashin kai, yayin da shi da Kwankwaso suke son shugabanci mai kawo sauyi wanda zai fitar da mutane daga talauci tare da inganta rayuwarsu.
Peter Obi ya bayyana cewa shi da Kwankwaso sun haɗu a ƙarƙashin jam'iyyar NDC bayan rikice-rikicen cikin gida da shari'o'i da suka dabaibaye ADC, inda suka yanke shawarar kafa sabon dandamalin siyasa domin tunkarar zaɓen 2027.
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ba su haɗa kai kafin zaɓen 2023 ba, Obi ya ce ba ya son komawa baya, domin hankalinsa yana kan makomar Najeriya da abin da zai amfani al'umma.
Ya kuma yi watsi da fargabar cewa haɗa magoya bayan Obidient da Kwankwasiyya zai haifar da rabuwar kai. A cewarsa, dukkan bangarorin suna da buri iri ɗaya na ganin an samu sabuwar Najeriya mai ci gaba da walwalar jama'a.
Buba Galadima: "Akwai Kalubale kan Tikitin Obi, Kwankwaso"
An ji cewa jigo a jam'iyyar NDC, Buba Galadima ya ce ana fuskantar ƙalubale wajen tabbatar da tikitin haɗin gwiwar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a 2027.
Ya yi wannan jawabi ne jim kadan bayan bayanan da ya yi a baya game da dalilan da suka jawo aka hada kai tsakanin manyan yan siyasar.
Injiniya Buba Galadima ya kuma buƙaci a daina ɗora wa Peter Obi laifin juyin mulkin soja na shekarar 1966 da aka yi a kasar nan saboda ba hannunsa.
Asali: Legit.ng


