Ministan PDP Ya Fadi Abin da Ya Sa Peter Obi Ya Doke Tinubu a Legas a Zaben 2023

Ministan PDP Ya Fadi Abin da Ya Sa Peter Obi Ya Doke Tinubu a Legas a Zaben 2023

  • Musliu Obanikoro ya yi ikirarin galabar LP a kan APC a jihar Legas a zaben 2023 ba ta da nasaba da karbuwar Peter Obi
  • Ya bayyana cewa tsoron da Kiristoci ke da shi na cewa za a mayar da su saniyar ware ne ya sa Bola Tinubu ya rasa Legas
  • Obanikoro ya kare Tinubu da cewa shi ba mai tsananin kishin addini ba ne, inda ya buga misali da matarsa da kuma ‘dansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Musiliu Obanikoro ya bude babin zaben shugaban kasa da aka yi a zaben 2023, inda Bola Ahmed Tinubu ya sha kunya a gida.

A babban zaben da ya gabata, Peter Obi da ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP ya yi galaba a kan har Bola Ahmed Tinubu.

Bola Tinubu
Bola Tinubu lokacin kamfe da Peter Obi wajen yakin zaben LP Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Musiliu Obanikoro ya fadi silar nasarar LP a Legas

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa: 'Tinubu ya fitar da mara 'da kunya, ya kamata a saka masa a 2027'

Musiliu Obanikoro wanda ya yi ministan tsaro a gwamnatin Goodluck Jonathan ya yi bayanin abin da ya faru a hirarsa a Mic On.

Obanikoro ya ce ba farin jinin Peter Obi ko jam’iyyar LP ta jawo wa Tinubu matsala ba, an tsorata da tikitin Musulmi da Musulmi ne.

‘Dan siyasar ya fada wa Seun Okinbaloye a shirin nasa cewa wasu sun tsorata da abin da zai faru da kiristoci idan aka zabi APC.

Ganin shi Tinubu musulmi kuma ya dauko musulmi a matsayin abokin gaminsa, Obanikoro ya ce sai wannan ya taimaki 'yan LP.

Idan aka duba Punch, za a ga ‘dan siyasar yana cewa kiristoci sun ji tsoron za a maida su saniyar ware ne idan APC ta ci zaben 2023.

Tinubu
Bola Tinubu lokacin yakin neman zaben APC Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tikitin Tinubu/Shettima ya tsora kiristoci

Ambasada Obanikoro yake bayani:

“Bari in fada maka, abin da ya kada mu a Legas shi ne tikitin Musulmi da Musulmi ba Peter Obi ba.
"Mutane sun ji tsoro, ba su san ya mulkin Bola Tinubu zai kasance ba.
“Jama sun dauka zai zama an yi watsi da Kiristoci a Najeriya, kuma an yi maganin wannan domin Tinubu ba mai tsauttsauran ra’ayi ba ne da zai fifita wani addini a kan wani."

Kara karanta wannan

Buba Galadima: "Akwai kalubale kan tikitin Obi da Kwankwaso"

Tinubu yana da tsattsauran ra'ayin addini?

Tsohon ‘dan takarar gwamnan ya nuna saukin ra’ayin Tinubu tun a cikin gidansa da yake zaune da Kiristoci alhali shi yana Musulmi.

Obanikoro yake cewa:

“Matarsa fasto ce. ‘Dan sa Seyi Kirista ne. A musulmi aka haife shi. Ya zama Kirista. Mafi yawan mutanen da ke cikin gwamnatinsa Kiristoci ne,”

Obanikoro bai kawo wasu alkaluma da za su nuna Kiristoci sun fi Musulmai yawa a cikin gwamnatin da Tinubu yake jagoranta ba.

Ekiti za ta yi wa Tinubu ruwan kuri'u

An rahoto Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ziyara a fadar Aso Rock bayan ya lashe zaben gwamna.

Yayin ziyarar, gwamnan ya yi wa Tinubu alwashin cewa mutanen Ekiti za su marawa APC baya tare da ba ta kuri'u tsakanin 600,000 zuwa 700,000 a 2027.

Gwamna Oyebanji ya kuma bayyana cewa nasarar da ya samu ta ta'allaka ne ga falalar Ubangiji da kuma goyon bayan da shugaban kasa ya ba shi a ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng