Shirin 2023: Hotuna sun bayyana, Tinubu ya kaddamar da Shettima a Abuja

Shirin 2023: Hotuna sun bayyana, Tinubu ya kaddamar da Shettima a Abuja

  • Jiga-jigan jam'iyyar APC sun taru a dakin taro na Shehu Musa 'Yar Adua domin kaddamar da abokin takarar Tinubu a zaben 2023
  • A tun farko, Bola Ahmad Tinubu ya zabe Sanata Kashim Shettima domin yin takara tare dashi a zaben 2023 mai zuwa
  • An samu cece-kuce daga 'yan Najeriya da dama kasancewar Tinubu da Shettima dukkaninsu Musulmai ne kuma za su yi takara tare

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki da dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu a hukumance sun kaddamar da Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an gudanar da bikin kaddamar da Shettima ne a dakin taro na Shehu Musa Yar’adua da ke Abuja, a ranar Laraba, 20 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

2023: Sabon sabani ya kunno kai a APC kan wanda Tinubu ya zaba mataimaki, Gwamna El-Rufa'i ya fusata

Tinubu ya kaddamar da Shettima a Abuja
Tikitin Musulmi/Musulmi: Hotunan lokacin da Tinubu ke tabbatar da zabo Shettima abkin takara | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta tattaro, bikin ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti.

Hakazalika, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi da Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno da Gwamna Abdullahi Ganduje Jihar Kano duk sun hallara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran wadanda suka halarci bukin kaddamarwar sun hada da Iyiola Omisore, sakataren jam’iyyar APC na kasa, da wasu manyan baki.

Hakan na zuwa ne makwanni biyu kacal bayan da dan takarar shugaban kasar ya zabi dan sanatan a matsayin abokin takararsa na zaben 2023.

Kalli hotunan:

Tinubu ya kaddamar da Shettima a Abuja
Tikitin Musulmi/Musulmi: Hotunan lokacin da Tinubu ke tabbatar da zabo Shettima abkin takara | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Tinubu ya kaddamar da Shettima a Abuja
Tikitin Musulmi/Musulmi: Hotunan lokacin da Tinubu ke tabbatar da zabo Shettima abkin takara | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kuka akan zabin Shettima da Tinubu yayi

Idan baku manta ba, zaben Shettima a makwannin baya na yin takara da Tinubu ya haifar da cece-kuce daga wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC, kungiyoyin fafutuka, kungiyoyin addini da sauran masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Abokin takara: A karshe APC ta sa ranar da Tinubu zai kaddamar da Shettima

Musamman malaman addini da kungiyoyin Kiristoci ta Najeriya ciki har da CAN da PFN sun nuna adawa da wannan zabe.

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa, wasu jiga-jigan jam'iyyar a fadin tarayyar kasar nan da dama sun fice daga jam'iyyar suna masu zargin Tinubu da rashin bin tafarkin dimokuradiyya.

Abokin takara: A karshe APC ta sa ranar da Tinubu zai kaddamar da Shettima

A tun farko, dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya tsaida sabon lokacin da zai gabatar da Kashim Shettima.

Punch ta kawo rahoto a ranar Talata. 19 ga watan Yuli 2022, da ya tabbatar da cewa a gobe Laraba Asiwaju Bola Tinubu zai kaddamar da Kashim Shettima.

Hakan na zuwa ne kwanaki kusan goma da ‘dan takaran na APC ya zabi Sanata Kashim Shettima. Sanarwar gabatar da ‘dan takarar mataimakin shugaban kasar ya fito ta bakin sakataren gudanarwa na jam’iyya mai mulki watau Suleiman Argungu.

Kara karanta wannan

Shettima: Yan Najeriya Sun Tattare Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Ke Kara Azama a Bangaren Fasaha

Asali: Legit.ng

Online view pixel