Obanikoro ya yi murnar sauya sheƙa ta ɗan sa zuwa APC
A ranar Juma'ar da ta gabata ne, Mista Babajide Obanikoro, ɗa ga tsohon ƙaramin minitsan tsaro, Sanata Musiliu Obanikoro, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa jam'iyyar APC.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, tun a watan Nuwamba na shekarar 2017 da ta gabata ne Sanata Musuliu ya yi wanka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Legit.ng ta fahimci cewa, ɗan sa Babajide, wanda yayi takarar shugaban karamar hukuma ta mazabar Ikoyi da Obalende, ya sha kashi har a karo biyu a karkashin tsohuwar jam'iyyar sa ta PDP.
KARANTA KUMA: Gwamnonin APC 14 da suka gana da shugaba Buhari a garin Daura
Shugaban jam'iyya na mazabar Ikoyi Mista Suleiman Yusuf, shine ya tarbi Babajide zuwa jam'iyyar ta APC tare da tsohon kwamshinan kudi na jihar, Mista Wale Edun.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, rikicin APC ya ƙara zurfafawa a yayin da wata ƙungiya ta jam'iyyar ta huro wuta don ganin an tsige shugaban jam'iyyar, Cif John Odigie-Oyegun, tare da kai ƙorafi har ga hukumar EFCC.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng