Zaben 2027: An Yi Hasashen Gwamnan da Zai Lallasa Shugaba Tinubu

Zaben 2027: An Yi Hasashen Gwamnan da Zai Lallasa Shugaba Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • Jam'iyyar Allied People’s Movement (APM) ta ce dan takararta, Gwamnan Oyo Seyi Makinde, zai doke Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027
  • APC mai mulki a Najeriya ta yi watsi da ikirarin, tana mai cewa ba shi da tushe
  • Kalaman sun zo ne yayin da ake samun sauye-sauyen kawance a siyasar Najeriya gabanin babban zabe na gaba

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Oyo - Jam’iyyar Allied People’s Movement (APM) ta ce dan takararta na shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, zai kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027.

Sai dai jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana wannan ikirari a matsayin abin da ba zai yiwu ba.

APM ta yi magana kan Makinde
Gwamna Seyi Makinde a wajen karbar tutar jam'iyyar APM Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Sakataren yada labarai na kasa na APM, Abubakar Yusuf, ya bayyana hakan yayin da yake magana da jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Rigimar takara tsakanin mutanen gwamnonin APC da shugabannin jam'iyya ta tafi kotu

Meyasa Makinde zai kifar da Tinubu?

Abubakar Yusuf ya ce jam’iyyar na da yakinin cewa Makinde yana da kwarewar shugabanci da karbuwa a fadin kasa da ake bukata domin kayar da Tinubu a 2027.

Ya bayyana cewa APM ta kara kaimi wajen wayar da kan jama’a da tattara magoya baya a fadin kasar, yayin da ake samun karuwar mambobin jam’iyyar bayan shigowar wasu fitattun ‘yan siyasa.

“Dan takarar shugaban kasar APM yana da kwarewar shugabanci, jajircewa da cancantar tunkarar kalubalen tsaro na Najeriya, farfado da tattalin arziki da kuma samar da amfanin shugabanci nagari."
“Sunan dan takararmu wajen kula da dukiyar jama’a cikin taka-tsantsan, shugabanci na gari da kuma jagoranci mai bai wa kowa dama zai zama ginshikin gwamnatin tarayya karkashin APM."
"Kwarewarsa, kuzarin samartaka da kuma iya hada kan ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da bambancin siyasa, kabila ko addini ba, ya sa muke da yakinin cewa yana da abin da ake bukata domin lashe zaben shugaban kasa na 2027."

Kara karanta wannan

An taso Tinubu a gaba game da lafiyarsa kan sake neman takara a 2027

- Abubakar Yusuf

Gwamna Makinde ya samu karbuwa

A cewar Abubakar Yusuf, jam’iyyar ta samu wasu fitattun ‘yan siyasa, yana mai bayyana hakan a matsayin shaida cewa jama’a na kara yarda da tsarin jam’iyyar.

Mai magana da yawun jam’iyyar ya ce ‘yan Najeriya na kara nuna rashin gamsuwa da halin da tattalin arziki da tsaro ke ciki, yana mai cewa APM na samar da wata sahihiyar madadin siyasa.

Ya bayyana Makinde a matsayin daya daga cikin gwamnonin da suka fi samun nasara a kasar, yana mai cewa irin ayyukan da ya yi a Jihar Oyo sun sa ya samu karbuwa a matakin kasa tare da kara karfin gwiwa kan ikonsa na mulkar Najeriya.

An yi hasashen Makinde zai samu nasara a zaben 2027
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo Hoto: Seyi Makinde
Source: Twitter

APC ta yi watsi da ikirarin

Sai dai APC ta yi watsi da kyakkyawan fata na jam’iyyar adawa, tana mai cewa Tinubu na kan hanyar samun wa’adi na biyu.

Daraktan yada labarai na APC, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa Gwamna Makinde ba ya kawo wata babbar barazana ta fuskar zabe ga Shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi yadda Kiristoci suka karbi tikitin Muslim Muslim a Najeriya

Ya ce sauye-sauyen Tinubu, wadanda aka fara suka tun farko, sun fara haifar da sakamako mai kyau, wanda ‘yan Najeriya za su fahimta tare da amincewa da shi kafin zabe na gaba.

Masu neman takara a APC za su gana da Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu daga cikin 'yan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Oyo da ba su gamsu da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani ba.

Fusatattun masu neman takarar sun amince za su karɓi duk wata gayyata daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin warware rikicin da ya biyo bayan zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng