Rikici a APC: Fusatattun Masu Neman Takara a Oyo za Su Zauna da Tinubu
- Wasu daga cikin wadanda su ke neman takarar gwamna a jam'iyyar APC reshen jihar su na ci gaba da nuna rashin jin dadinsu a kan zaben fitar da gwani
- Duk da cewa an kafa kwamitin sulhu a jam'iyyar, kuma har ya fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin sasanta rikicin, da alama lamarin ya girmama
- Sai dai masu neman takarar sun ce za su ci gaba da zama a APC duk da rashin jin dadinsu kan zaben yayin da shugaban kasa Bola Tinubu ya kira su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Oyo – Wasu daga cikin 'yan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Oyo da ba su gamsu da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani ba.

Kara karanta wannan
Bauchi: Bala Mohammed ya yi garambawul a majalisar zartarwa, ya sauke kwamishinoni 2
Fusatattun masu neman takarar sun amince za su karɓi duk wata gayyata daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin warware rikicin da ya biyo bayan zaben.

Source: Twitter
Jaridar Guardian ta wallafa cewa matsayar ta fito ne bayan tarukan tuntuba da Kwamitin Sulhu kan zaben fidda gwamnan APC a jihar Oyo ya gudanar da su domin sasanta rikicin da kuma ƙarfafa haɗin kan jam'iyyar kafin zabuka masu zuwa.
Bola Tinubu zai ga masu neman takara
Jaridar The Nation ta kawo labarin cewa a cikin sanarwar bayan taron da shugabannin kwamitin, Sanata Olufemi Lanlehin da Farfesa Taoheed Adedoja suka sanya wa hannu, an bayyana cewa tattaunawar na cikin aikinsu.
Kwamitin ya ce ya gana da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Injiniya Rauf Aderemi Olaniyan, Prince Asatola Ashanke, Dakta Ololade Usman Bakare, Injiniya Oyedele Hakeem Alao da Dakta Ayobami Lam-Adesina a tarukan da aka gudanar a ranar 8 da 10 ga Yulin 2026.
Haka kuma, kwamitin ya bayyana cewa wani ɗan takarar gwamna, Dakta Adewale Kolapo Kareem, ya riga ya bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar gwamna na APC.
Masu neman takara a APC sun fusata
Sanarwar ta ce masu neman takarar sun nuna rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da zaben fidda gwamnan, inda suka nuna damuwa kan tsarin zaben da kuma sakamakon da aka samu.

Source: Facebook
Sai dai duk da korafe-korafen da suke da su, sun sake jaddada biyayyarsu ga APC tare da alƙawarin ci gaba da tattaunawa da kwamitin sulhu domin samun mafita mai ɗorewa.
A cewar sanarwar, masu neman takarar sun cimma matsaya guda cewa za su amsa duk wata gayyata daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin tattauna matsalolin da suka taso da nufin kawo ƙarshen rikicin.
Sanarwar ta ce:
"A matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa sulhu, masu neman takarar sun amince baki ɗaya cewa za su karɓi duk wata gayyata daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin tattauna korafe-korafensu da kuma warware matsalolin gaba ɗaya."
Gwamnatin Tinubu ta je kotu
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta gurfanar da wasu mutum uku kan zargin hannu a sace dalibai da malamai a Oriire da ke jihar Oyo lamarin da ya jawo tasgaro a ilimin yaran.
Ana tuhumar su da aikata ta'addanci, boye bayanan 'yan ta'adda, tunzura jama'a da hakar zinari ba bisa ka'ida ba yayin da ake sa ran kotu za ta dauki matakin da ya dace wajen hukunta su idan an same su da laifi.
Takardun karar sun nuna cewa tsakanin watan Janairu zuwa Mayun 2026, wadanda ake zargin sun hada baki da wasu mutum uku da suka hada da Muhammad Sani, Jibril Mohammed da Ibrahim Khabab sun aikata ta'addanci.
Asali: Legit.ng
