Kashin 'Yan Bindiga Ya Bushe, Gwamnati Ta Bullo da Dabarun Yaki da Ta'addanci a Najeriya

Kashin 'Yan Bindiga Ya Bushe, Gwamnati Ta Bullo da Dabarun Yaki da Ta'addanci a Najeriya

  • Fadar shugaban kasa ta bayyana dabarun da gwamnatin tarayya ke amfani da su wajen kawar da ayyukan ta'addanci a Najeriya
  • Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya ce gwamnati za ta tura masu gadin dazuka domin hana 'yan ta'adda fakewa da satar albarkatun kasa
  • Ya jaddada cewa ana amfani da jiragen yaki marasa matuki da sauran fasahohin zamani wajen sa ido kan masu laifi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana wasu muhimman matakan da gwamnatin tarayya ke dauka domin kawo karshen matsalar tsaro.

Bwala ya ce gwamnatin Najeriya na ci gaba da daukar tsauraran matakai domin kawar da ta'addanci, fashi da makami da garkuwa da mutane a fadin Najeriya.

Tinubu da Bwala.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da da hadiminsa, Daniel Bwala a Aso Rock Hoto: @bwaladaniel
Source: Twitter

Daniel Bwala ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin The Link Up Podcast, wanda echoRoom ta shirya.

Kara karanta wannan

Mutane sun kone kurmus da motar gas ta fashe a kusa da sojoji

Wane dabaru aka bullo da su?

Bwala ya ce gwamnati na kara daukar jami'an tsaro tare da sake horas da su, saboda adadin jami'an da ake da su bai isa ba idan aka kwatanta da yawan jama'a da girman kasar.

Ya ce:

"Muna zuba jari wajen horaswa da sake horaswa. Haka kuma muna kara daukar jami'an tsaro saboda wadanda muke da su ba su isa ba idan aka kwatanta da yawan jama'a da fadin kasar."

Ana shirin tura masu gadin dazukan Najeriya

A cewarsa, wasu daga cikin sababbin jami'an za su yi aiki a matsayin masu gadin dazuka domin hana 'yan ta'adda amfani da dazuka wajen boyewa da kuma satar albarkatun kasa.

Ya kara da cewa ana kara yawan jami'an 'yan sanda, sojoji, DSS da jami'an tsaron ruwa domin inganta tsaro, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Gwamnati na amfani da fasahar zamani

Bwala ya ce gwamnatin tarayya na amfani da fasahohin zamani kamar jiragen yaki marasa matuki da na'urorin tattara bayanan sirri domin gudanar da sa ido ba dare ba rana.

Kara karanta wannan

Amurka ta kara taso Najeriya a gaba game da kare rayukan kiristoci

Ya ce:

"Muna zuba jari a fasahohin zamani da ke taimaka mana wajen sa ido ko da muna barci, ciki har da jiragen yaki marasa matuki da na'urorin tattara bayanan sirri."
Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, babban kwamandan askarawan Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Mai bai wa shugaban kasa shawarar ya bayyana cewa garkuwa da mutane ta zama wani "rikicin tattalin arziki", inda ya ce ba 'yan ta'adda kadai ke aikata irin wadannan laifuka ba.

A cewarsa, wasu lokuta ma makwabta ko mutanen da suka san wadanda aka sace ne ke da hannu a lamarin.

Fadar shugaban kasa ta soki Gwamna Makinde

Kun ji cewa fadar shugaban kasa ta soki Gwamna Seyi Makinde kan bukatar binciken Majalisar Dinkin Duniya (UN) game da sace dalibai da malamai a Oyo.

Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce jami'an tsaro sun riga sun yi bayanin yadda aka kubutar da wadanda aka sace, don haka babu bukatar wani bincike na waje.

Sai dai ya tambayi dalilin wannan bukata, yana mai cewa babu wata hujja da za ta sa jami'an tsaro su jefa 'yan Najeriya, musamman kananan yara, cikin irin wannan wahala da gangan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262