Jagoran Matasan Kwankwasiyya Ya Koma Tafiyar Gwamna Abba, Dankabo Ya Yi Martani
- Hon. Fahad Dankabo ya yi maraba da Sadeeq Garo bayan sauya shekarsa zuwa APC, yana mai bayyana cewa matasa irinsa ne Kano ke bukata
- Dankabo ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta mayar da Kano cibiyar kasuwanci, tattalin arziki da al'adu a Najeriya da Afrika ta Yamma
- A wata sanarwar da ya fitar, Sadeeq Garo ya bayyana babban dalilin da ya sanya bar jam'iyyar NDC ta su Sanata Rabiu Kwankwaso zuwa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Tsohon mai neman takarar kujerar Majalisar Wakilai a mazabar Gwarzo da Kabo a jihar Kano, Hon. Fahad Muhammad Dankabo, ya yi maraba da Sadeeq Garo bayan sauya shekarsa daga jam'iyyar NDC zuwa APC.
Fahad Dankabo ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya yaba wa jagoran matasan Kwankwasiyyar tare da nuna cikakken goyon bayansa ga gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Source: Facebook
'Kano na bukatar matasa masu kishi' - Dankabo
A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dankabo ya bayyana cewa Sadeeq Garo na daga cikin matasan da Kano ke bukata saboda jajircewarsa da kishinsa na ci gaban al'umma.
Ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta farfado da martabar Kano ta fuskar al'adu, ci gaban tattalin arziki, masana'antu da kuma fasahar zamani.
A cewarsa, Gwamna Abba zai mayar da Kano matsayin cibiyar kasuwanci, al'adu da tattalin arziki ba kawai a Najeriya ba, har ma a yankin Afrika ta Yamma.
Dankabo ya kuma tabbatar wa Sadeeq Garo cewa shi da sauran masu irin wannan buri za su ci gaba da samun goyon baya wajen ganin an samu ingantaccen shugabanci da ci gaban al'umma.
Ana so Garo ya ci gaba da ba APC gudunmawa
Tsohon mai neman takarar ya bukaci sabon dan APC din da ya ci gaba da kokarin ganin Kano ta samu ci gaba karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan
Dalilin da ya sa Bala Adamu ya amince ya zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a 2027
Ya ce yana da yakinin cewa makomar jihar za ta kasance mai kyau idan aka ci gaba da hada kai da kuma tallafa wa manufofin gwamnatin jihar.
Dalilin sauya shekar Sadeeq Garo

Source: Facebook
Sadeeq Garo ya sanar a shafinsa na Facebook cewa ya bar jam'iyyar NDC domin komawa APC bayan dogon tunani da nazari kan makomar siyasarsa.
"Wannan sauya sheka tawa ta faru ne ƙarƙashin jagorancin babban gigo kuma jajirtaccen jagora, Hon. Fahad Muhammad Adamu Dankabo, tsohon ɗan takarar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Gwarzo da Kabo.
"Ina son in fahimtar da daukacin masoya da masu biyo bayanmu cewa, barin jam'iyyar NDC ba yana nufin na bar tsarin Kwankwasiyya ba ne baki ɗaya. Tsarin Kwankwasiyya tunani ne na ci gaban al'umma, kuma muna nan a kai."
- Sadeeq Garo.
Burin Dankabo na yin takara a APC
Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa, Hon. Fahad Dankabo ya ayyana neman takarar kujerar wakilin Gwarzo da Kabo a Majalisar Wakilai ta tarayya karkashin APC.
Fahad Dankabo ya bayyana cewa ya yarda ya nemi takarar ne bayan matsin lamba daga al’umma da kuma shawarwarin jiga-jigan siyasarsa.
Mai neman takarar ya yi alkawarin karkata akalar wakilcin sa wajen inganta ilimi, tallafawa mata da matasa, da kuma samar da ababen more rayuwa.
Asali: Legit.ng
