Kujerun Mata: Alamu Sun Nuna Za a Kara Yawan Sanatoci da Yan Majalisar Wakilai a Zaben 2027
- Da yiwuwar a kara kujerun Majalisar Dokoki ta Kasa daga 469 zuwa 518 idan har kudirin ware wa mata wani kaso ya zama doka a Najeriya
- Karin kujeru 49 da za a samu a Majalisar dattawa da ta wakilai za a ware su ne musamman domin mata
- Rahoto ya nuna cewa da yiwuwar sanatoci za su karu daga 109 zuwa 121, yayin da 'yan Majalisar Wakilai za su tashi daga 360 zuwa 397
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Alamu sun nuna cewa yawan kujerun Majalisar Dokoki ta Kasa zai karu idan aka amince da wani kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kara yawan wakilcin mata a harkokin mulki.
Idan kudirin ya zama doka, kujerun Majalisar Dattawa za su karu daga 109 zuwa 121, yayin da kujerun Majalisar Wakilai za su tashi daga 360 zuwa 397, tun daga babban zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: An cafke wasu yan ƙasashen waje kan zargin hannu a matsalar tsaron Najeriya

Source: Facebook
Za a ware sababbin kujeru ga mata
Rahoton Leadership ya nuna cewa sababbin kujeru 12 na Majalisar Dattawa da kuma kujeru 37 na Majalisar Wakilai za a ware su ne musamman ga mata.
An sake nuna goyon baya ga kudirin ne a wani taron mata da kungiyar League of Women Voters of Nigeria (NILOWV) ta shirya tare da masu daukar nauyin kudirin.
Daya daga cikin masu daukar nauyin kudirin, Hon. Iduma Igariwey Enwo, ya ce shugabannin Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun nuna goyon baya ga kudirin, amma ya bukaci a ci gaba da fafutuka domin tabbatar da amincewa da shi.
Ya ce:
"Ni da wasu mambobin Majalisar Wakilai mun dade muna fafutukar ganin mata sun samu karin damar shiga shugabanci. Saboda haka muna goyon bayan wannan kudiri."
Za ta bude wa mata karin dama
Igariwey ya ce tsarin zai bai wa mata damar shiga Majalisar Dokoki ta Kasa da majalisun jihohi, wanda daga bisani zai ba su damar fafatawa a zabukan gama-gari.

Kara karanta wannan
An koma gidan jiya; ‘yan kasuwan da suka shigo da mai sun yi kara kudin fetur daga N1200
Sai dai ya jaddada cewa dole ne a kara wayar da kan mambobin majalisun dokokin jihohi 36, domin amincewarsu na da matukar muhimmanci wajen gyaran kundin tsarin mulki.
Yadda za a raba kujerun mata a Najeriya
Babban Daraktan cibiyar African Parliamentary Resource Centre (APRC), John Ebikeseye, ya bayyana cewa kujeru 12 na Majalisar Dattawa za a raba su daidai tsakanin yankuna shida na siyasa, inda kowanne zai samu sanatoci mata biyu.
Ya kuma ce kujeru 37 na Majalisar Wakilai za a bai wa kowace jiha kujera daya, yayin da FCT ita ma za ta samu kujera daya, kamar yadda The Sun ta ruwaito.

Source: Facebook
A cewarsa, za a zabi masu rike da wadannan kujeru ne ta hanyar killataccen zabe da zao kunshi zababbun kansiloli, shugabannin kananan hukumomi da mataimakansu.
Tinubu ya watsawa majalisa kasa a ido
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya ƙi amincewa da kudurori biyu da Majalisar Tarayya ta amince da su saboda kura-kurai da suka saɓa wa kundin mulki.
Duk da ƙin amincewar da ya nuna, Tinubu ya bayyana cewa zai iya rattaba hannu kan kudurorin idan Majalisar Tarayya ta gyara matsalolin da ya nuna.
Asali: Legit.ng