Pantami: Da Mu Zabi ‘Dan Izala gara Mu Zabi Kirista In ji Malamin Darikar Tijjaniya
- Alhaji Ali ya yi wa’azi yana gargadin mabiya darika a kan goyon bayan ‘yan Izala a lokacin takara
- Malamin ya ce gara su kada kuri’arsu ga Kirista ko Arna a kan su goyi bayan irinsu Ali Pantami
- A matsayinsa na shehin Tijjaniya, ya ce duk wanda ya bi bayan mabiya Izala, ya yi sallama da Shehu Tijjani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Adamawa - Wani malamin addini a Arewacin Najeriya ya gargadi mabiyansa game da irin mutanen da za su zaba.
Ana zargin malamin ya yi wannan jan-kunne ne ganin nan da ‘yan watanni kadan za a buga gangar siyasa a kasar nan.

Source: Facebook
Malamin Tijjaniya ya ce a guji 'yan Izala
Wani bidiyo a shafin Ibrahim Badamasi Yunusa ya Facebook ya nuna Sheikh Alhaji Ali yana sukar zaben ‘dan Izala.

Kara karanta wannan
Peter Obi, Kwankwaso, Binani da fitattun ‘yan siyasa 10 da suka rabu da hadakar ADC
Sheikh Alhaji Ali ya yi wa’azi yana mai cewa gara su zabi kowane irin mutum a kan wadanda suke cikin kungiyar Izala.
A matsayinsa na malamin Musulunci, ya fada wa almajiransa gara su goyi bayan kirista a kan ‘dan Izala a zabe.
“Da mu zabi ‘dan Izala gara mu zabi kirista. Da mu zabi ‘dan Izala gara mu zabi gara mu zagi arne.
“Da mu zabi ‘dan Izala gara Musulmi kowane irin Musulmi. Wane ne ba ba za mu zaba ba a Najeriya? Shi ne ‘dan Izala.”
- Sheikh Alhaji Ali
An ce 'yan Tijjaniya su guji Isa Pantami
Baro-baro malamin ya shaida cewa babu ruwansu da takarar Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami da Sanata Buba Umar Shehu.
Isa Pantami yana takarar gwamna a Gombe a jam’iyyar PDP shi kuma Sanata Buba ya shiga PRP yana takara a Bauchi a 2027.
Ana ganin wadannan 'yan siyasa suna da kusanci da kungiyar Izala da aka kafa a Najeriya a 1978.
Sheikh Alhaji Ali ya ce:

Kara karanta wannan
Dalilin Atiku na jawo Amaechi su yi takarar shugaban kasa tare a ADC ya fito fili
“’Dan Izala ba za mu zabe ka ba, Pantami ba zamu zabe ka ba. Buba Shehu ba za mu zabe ka. Ire-irenku kaf ba za mu zabe ku ba.”
Gargadi da 'yan darikar Tijjaniya
Malamin ya yi rantsuwa yana cewa duk wani dan darika da ya biye wa son rai ya zabe su, ya raba jiha da Shehu Ahmadu Tijjani.
Alhaji Ali ya fadakar da ‘yan Tijjaniya cewa duk wanda ya yarda ya zauna da makiyin Shehu Tijjani, to ya rabu da darikarsa kenan.
Domin kara fito da misalinsa fili, ya ce babu dan halas da zai zauna a wurin da ake zagin ubansa, sai dai idan ‘dan na shege ne.
Isa Pantami ya shiga coci a Gombe
Wani rahoto ya zo da labarin ziyarar da tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya kai wa wani coci a ECWA a garin Gombe.
Sheikh Pantami ya ziyarci cocin ECWA da ke Federal Low-Cost a garin Gombe ne domin yi musu jaje game da gobarar da ta faru a majami'arsu.
'Dan takarar gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin PDP ya kai ziyarar ne a matsayin wakilin jagoran jam'iyyar a Gombe, Sanata Ibrahim Dankwambo.
Asali: Legit.ng