Yan Bindiga Sun Kwashe Ƴan Gida Ɗaya yayin da Suka Dauke da Gawar Mahaifiyarsu

Yan Bindiga Sun Kwashe Ƴan Gida Ɗaya yayin da Suka Dauke da Gawar Mahaifiyarsu

  • Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wasu 'yan uwa har mutane uku da ke raka gawar mahaifiyarsu domin jana'iza
  • Mazauna yankin sun ce sun ji karar harbe-harbe da misalin karfe 3:00 zuwa 4:00 na asubahin ranar Asabar
  • Shugaban karamar hukumar Ohimini a Benue ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya nuna alhini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makurdi, Benue - An ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun sace 'yan uwa uku da ke kai gawar mahaifiyarsu domin a yi mata jana'iza.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Ohimini da ke jihar a Benue wanda ya tayar da hankalin al'ummomin yankin.

Yan bindiga sun sace ƴan gida ɗaya a Benue
Rundunar sojojin Najeriya da Gwamna Alia Hyacinth. Hoto: HQ Nigerian Army, Fr. Alia Iormen Hyacinth.
Source: Facebook

Rahotanni daga Tribune sun ce satar ta faru ne da misalin karfe 4:00 na asubahin ranar Asabar 18 ga watan Yulin 2026.

Yan sace ƴan gida ɗaya a Benue

Kara karanta wannan

Iyalan budurwar da aka tsinci gawarta a gidan ministan Tinubu sun kai ƙorafi gaban IGP

Yan uwan suna kan hanyarsu ta zuwa garin Iklenyi da ke karamar hukumar Okpokwu, an ce masu garkuwar sun tare su ne tsakanin Omutele da Ankpechi a kan titin Ogobia zuwa Otukpo, cikin gundumar Oglewu ta karamar hukumar Ohimini.

Wani mazaunin Omutele mai suna Elijah ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho cewa mazauna yankin sun ji karar harbe-harbe tsakanin karfe 3:00 da hudu na asuba.

Ya ce da farko sun yi zaton makiyaya masu dauke da makamai ne suka kai hari kauyen, sai da gari ya waye suka gano cewa an sace matafiyan.

Elijah ya ce mutanen da aka sace suna raka gawar mahaifiyarsu daga Abuja zuwa Iklenyi domin a yi mata jana'iza a garinsu da ke Okpokwu.

Wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya yi zargin cewa motar da suke ciki ta samu matsalar inji, hakan ya sa suka makale a hanya kafin masu garkuwa su afka musu.

Yan bindiga sun sace ƴan gida ɗaya a Benue
Taswirar jihar Benue da ke fama da hare-haren ƴan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Shugaban karamar hukuma ya yi martani

Shugaban karamar hukumar Ohimini, Gabriel Adole, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa zai je wurin domin tantance abin da ya faru da cikakkun bayanai.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Benue, DSP Udeme Edet, ta ce har yanzu ba ta samu rahoton lamarin ba.

Kara karanta wannan

Kebbi: Yan bindiga sun bindige babban darakta, sun sace matarsa da malamar makaranta

Ta yi alkawarin bayar da karin bayani bayan samun rahoto daga jami'an yankin yayin da jihar ke fama da rashin tsaro, cewar Punch.

An tuna cewa a makon da ya gabata wasu 'yan bindiga sun kai hari kan jerin motocin da ke raka gawar marigayi mataimakin kwamandan FRSC, Augustine Ikwue, a Kogi.

Sun sace wasu matafiya tare da kwace gawar, kafin daga baya su watsar da ita aka dawo da ita domin jana'iza.

Matashi ya kashe Farfesa a Benue

Mun ba ku labarin cewa rundunar 'yan sandan Benue ta kama wani dan Arewa da ake zargin ya hallaka Farfesa da kannensa.

An kama matashin mai shekaru 23 bisa zargin hannu a kisan Farfesa Gabriel Nyityo a Makurdi da ke Benue.

Kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, ya ce jami'ai sun samu kiran gaggawa zuwa yankin Adaka inda suka tarar da gawarwakin Farfesa Nyityo da ƙanensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.