Trump Ya Fitar da Gargadin da Ya Shafi Iran, Rasha, Nijar da Kasashe 23 a Duniya
- Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanya ƙasashe 23 cikin matakin gargadi mafi girma na "kada a yi tafiya" zuwa cikinsu
- Ƙasashe 11 daga nahiyar Afirka na cikin jerin, yayin da Najeriya ta ci gaba da kasancewa a mataki na uku har yanzu
- Duk da cewa gargadin bai shafi Najeriya kai tsaye ba, Amurka ta ware wasu jihohin Najeriya da ta ce suna cikin hadari sosai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar da sabon gargaɗin tafiye-tafiye inda ta shawarci 'yan ƙasarta da kada su yi tafiya zuwa ƙasashe 23 da ta sanya a matakin haɗari mafi girma.
Hakan na zuwa yayin da Amurka ke takun saka da kasashe da dama da suka hada da Iran a Gabas ta Tsakiya da kasar Rasha.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa ma'aikatar ta bayyana cewa ana sanya ƙasa a wannan mataki ne idan yanayin tsaro ya yi muni ko kuma gwamnatin Amurka ba za ta iya ba da cikakken taimako ga 'yan ƙasarta da ke wurin ba.
Sanarwar ta ce:
"Mun fitar da gargaɗin tafiye-tafiye daga mataki na ɗaya zuwa na huɗu. Mataki na huɗu na nufin kada a yi tafiya ko kaɗan. Waɗannan wurare na da haɗari, saboda haka kada a je can saboda kowane irin dalili."
Waɗanne ƙasashe ne ke cikin jerin?
Jerin ƙasashen da Amurka ta sanya sun haɗa da:
- Afghanistan
- Belarus
- Burkina Faso
- Myanmar
- Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
- Chadi
- Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo
- Haiti
- Iran
- Iraq
- Lebanon
- Libya
- Mali
- Nijar
- Koriya ta Arewa
- Rasha
- Somalia
- Sudan ta Kudu
- Sudan
- Syria
- Uganda
- Ukraine
- Yemen
Daga cikin waɗannan, ƙasashe 11 na nahiyar Afirka sun haɗa da Burkina Faso, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Chadi, DR Congo, Libya, Mali, Nijar, Somalia, Sudan ta Kudu, Sudan da Uganda.

Source: Getty Images
Matsayin Najeriya a sabon gargaɗin
Amurka ta ci gaba da barin Najeriya a mataki na uku, inda ta shawarci 'yan ƙasarta da su sake yin nazari kafin su yi tafiya zuwa ƙasar.
Sai dai ta sanya wasu jihohin Najeriya a mataki na huɗu saboda matsalolin tsaro. Jihohin da ke Arewa sun haɗa da Borno, Jigawa, Kogi, Kwara, Neja, Filato, Taraba, Yobe da kuma Arewacin Adamawa.
Tribune ta wallafa cewa a Kudu kuma akwai jihohin Abia, Anambra, Bayelsa, Delta, Enugu, Imo da Rivers (ban da birnin Fatakwal).
Amurka ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne saboda matsalolin laifuka, ta'addanci, garkuwa da mutane, rikice-rikicen cikin gida da kuma rashin daidaiton ayyukan kiwon lafiya a wasu sassan Najeriya.
Tinubu ba fuskantar barazanar Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa wakilin dindindin na Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Ambasada Jimoh Ibrahim, ya wanke Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
Amurka ta sake karfafa Saudiyya ana tsaka da yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Jimoh Ibrahim ya musanta rahotannin da ke cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na fuskantar haɗarin kamu idan ya ziyarci Amurka.
Ambasada Ibrahim ya bayyanaj cewa babu wata hujjar doka da ke goyon bayan irin waɗannan ikirari, yana mai cewa Shugaba Tinubu zai halarci taron UNGA) ba tare da wata matsala ba.
Asali: Legit.ng

