Dubu Ta Cika: An Cafke Wasu Yan Kasashen waje kan Zargin Hannu a Matsalar Tsaron Najeriya

Dubu Ta Cika: An Cafke Wasu Yan Kasashen waje kan Zargin Hannu a Matsalar Tsaron Najeriya

  • Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa sojoji sun kama wasu 'yan kasashen waje da ake zargi da alaka da rashin tsaro
  • Hadimin shugaba Bola Tinubu, Daniel Bwala ya bayyana cewa ba a fitar da sunayen kasashen nasu ba saboda dalilan tsaro
  • Bwala ya ce gwamnatim tarayya na aiki tukuru domin hana Boko Haram da ISWAP bazuwa zuwa Kudancin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeiria - Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kama wasu yan kasashen waje da ake zargi da hannu a rura wutar matsalar tsaro.

Mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa, Daniel Bwala, ya ce ana zargin mutanen da haddasa matsalolin tsaro a wasu sassan Najeriya.

Bwala.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da hadiminsa, Daniel Bwala a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja Hoto: @BwalaDaniel
Source: Twitter

Bwala ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin The Link Up Podcast, wanda EchoRoom ta shirya.

Kara karanta wannan

Kashin 'yan bindiga ya bushe, gwamnati ta ɓullo da dabarun yaƙi da ta'addanci a Najeriya

Sojoji sun kama yan kasashen waje

Ya ce tsoma bakin wasu kasashen waje cikin harkokin Najeriya yana da nasaba da batutuwan tsaro da kuma muradun tattalin arziki, musamman albarkatun mai da wasu matakai da gwamnatin tarayya ta dauka a baya.

Ya ce:

"Idan za ku tuna, bayan wata muhimmiyar shawara da gwamnatin tarayya ta dauka, sai muka fara ganin wasu na daga tutocin Rasha a wasu sassan Najeriya."
"Dakarunmu sun kama wasu 'yan kasashen waje a tsakiyar Najeriya."

Gwamnati ta boye sunayen kasashensu

Bwala ya bayyana cewa rundunar soji ta ki bayyana kasashen da wadanda aka kama suka fito saboda dalilan tsaro da kuma ci gaba da tattaunawar diflomasiyya.

A cewarsa, gwamnatin Najeriya ta tuntubi kasashen da ake zargin mutanensu da hannu a lamarin.

Ya ce:

"Idan ka kama irin wadannan mutane, wani lokaci ana tsare su har sai kasarsu ta rike wani mutum da ake bukata, sannan a yi musayar fursunoni."

Kara karanta wannan

Masanin da ya yi tsayuwar daka yana kare Musulunci a Amurka ya rasu

Ya kara da cewa kasashen da ke da kyakkyawar alaka da Najeriya kan fi samun damar gyara matsalar cikin sirri maimakon a bayyana sunayensu a bainar jama'a.

Da aka tambaye shi ko Hukumar Leken Asirin Amurka (CIA) na da hannu wajen daukar nauyin ta'addanci a Najeriya, Bwala ya ce ba zai iya tabbatar da hakan ba.

Sai dai ya tuna cewa wani dan majalisar dokokin Amurka, Scott Perry, ya taba tayar da irin wannan batu yayin zaman majalisar kasar.

sojoji.
Dakarun rundunar sojin Najeriya a shingen binciken ababen hawa Hoto: Army
Source: Twitter

Boko Haram da ISWAP na kokarin bazuwa

Bwala ya ce Boko Haram da kungiyar ISWAP sun bazu daga Arewa maso Gabas zuwa Arewa maso Yamma, kuma yanzu suna kokarin shiga Arewa ta Tsakiya.

Ya ce gwamnati na daukar matakai domin dakile wannan yunkuri kafin ya kai yankunan Kudancin Najeriya, cewar rahoton Punch.

Gwamnatin Tinubu ta bullo da dabaru

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta bayyana dabarun da gwamnatin tarayya ke amfani da su wajen kawar da ayyukan ta'addanci a Najeriya.

Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya ce gwamnatin Najeriya na ci gaba da daukar tsauraran matakai domin kawar da ta'addanci, fashi da makami da garkuwa da mutane a fadin Najeriya.

Ya ce gwamnati na kara daukar jami'an tsaro tare da sake horas da su, saboda adadin jami'an da ake da su bai isa ba idan aka kwatanta da yawan jama'a da girman kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262