An Koma Gidan jiya; ‘Yan Kasuwan da Suka Shigo da Mai Sun Kara Kudin Fetur daga N1200
- Kamfanoni masu zaman kansu masu shigo da mai a Najeriya sun shirya tsaf don yin karin farashin fetur
- Babban abin da ya haifar da wannan mataki a kasuwa shi ne tsadar sauke man fetur daga kasashen waje
- Farashin lita a wuraren adana mai zai koma fiye da ₦1,300 a sakamakon rigimar da Amurka take yi da Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - ‘Yan kasuwa masu shigo da mai daga kasashen ketare sun fara yunkurin karin farashi saboda halin da ake ciki.
Bayan samun ragi kwanan nan, akwai yiwuwar nan da wasu ‘yan awanni a ji kudin da ke sayen litar man fetur ya canza.

Source: Getty Images
'Yan kasuwa sun canza kudin litar fetur
Jaridar The Cable ta ce ‘yan kasuwa za su kara farashin da ake saida lita a manyan tashoshi daga N1,230 zuwa N1, 350.
Tuni har ‘yan kasuwan sun sanar da abokan huldarsu cewa su shirya sayen kowace litar man fetur yanzu akalla a kan N1, 350.
Daga yau Juma’a, 17 ga watan Yuli 2026 ake sa ran cewa sabon farashin zai fara aiki, hakan na nufin za a ga sauyi a gidajen mai.
Mene ne ya jawo tashin kufin fetur?
An ji cewa farashin ya zama dole ne a sakamakon canjin da aka samu a kudin da ake sayen jirgin mai daga kasuwar duniya.
Hakan na zuwa ne bayan hukumar NMDPRA ta tarayya ta ba wasu kamfanoni lasisin shigo da fetur da dizil daga kasashen waje.
‘Yan kasuwan da aka zaba za su iya shigo da fetur da dizil daga ketare na tsawon watanni daga Yuli zuwa karshen Satumba.
Kamfanoni sun samu lasisin shigo da mai
Rahoton da aka samu daga Argus ya ce kamfanonin AA Rano, AYM Shafa, Bono, NIPCO da Pinnacle sun samu lasisin fetur.
Haka zalika AA Rano, AYM Shafa, Bono, Matrix da Pinnacle suna da damar da za su shigo Najeriya da dizil daga kasuwannin waje.

Kara karanta wannan
'Yan Arewa za su amfana da Amurka ta kawo tallafi mai kyau a fannoni 3 a Najeriya

Source: Getty Images
Ana tunanin bada lasisin shigo da mai zai karya farashin kaya sai kawai aka ji sanarwar kari a kudin da ake sayen man fetur a tashoshi.
Muddin manyan ‘yan kasuwa suka tashi farashi, babu makawa sai ‘yan sari sun canza kudin litar fetur ko kuwa su kwana a ciki.
Rikicin Amurka da Iran ya hana kasuwa sakat
Wani rahoto na jaridar Premium Times ya yi bayanin cewa takkadamar da ake samu a mashigar Hormuz yana jawo tsadar mai.
Duk yadda gwamnatin Najeriya ta so ganin sun saye man fetur da araha, hakan zai yi wahala idan Amurka suna rikici da kasar Iran.
Hana jiragen ruwan da suka dauko mai wuce wa salin-alin ta Hormuz ya dade yana taba masu wannan kasuwanci a fadin duniya.
Lokacin da aka rage kudin man fetur
A karshen 2025 aka ji matatar man Dangote ta fara sayar da litar fetur a kan ₦739 a dukkan gidajen mai na MRS Oil da ke faɗin Najeriya.
An ɗauki wannan matakin ne da nufin rage wa 'yan ƙasar wahalhalu tare da sauƙaƙa musu hidindimun lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.
Haka kuma, matatar ta gargaɗi masu yunƙurin ƙirƙirar ƙarancin mai don hana saukar farashin yin aiki, tare da yin kira ga 'yan kasuwa su yi koyi.
Asali: Legit.ng

