Majalisar Dattawa Ta Gabatar da Dokar da Ta Shafi Hana Wa'azi

Majalisar Dattawa Ta Gabatar da Dokar da Ta Shafi Hana Wa'azi

  • Majalisar Dattijai ta amince da gyaran dokar hukumar FRSC ta 2026 inda ta tsara tarar ₦50,000 ga masu talla ko wa'azi a motocin jigilar jama'a
  • Sabuwar dokar ta tanadi hukuncin tarar ₦50,000 ko ɗaurin watanni shida ga direbobin da suka ƙi ba da haɗin kai yayin binciken shan barasa
  • A zaman majalisar, an kuma ƙara tara daban-daban kan keta dokokin titi kamar gudun ganganci da dai sauran abubuwan da suka shafi FRSC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Majalisar Dattijan Najeriya ta amince da ƙudirin gyaran dokar hukumar FRSC na shekarar 2026, inda ta nemi a ci tarar ₦50,000 ga duk wanda aka kama da laifin talla, kasuwanci, ko wa'azi a cikin motocin haya.

Wannan ƙudiri, wanda yanzu haka ke jiran sa hannun shugaban kasa don zama doka, ya kuma tsara tarar ₦50,000 ko ɗaurin watanni shida, ko duka biyun, ga direbobin da suka ƙi amincewa a gwada su don sanin ko sun shan kayan maye.

Kara karanta wannan

Gwamna ya zakulo samari da zawarawa 300, zai masu auren gata da sadakin N250000 a Kebbi

Yan majalisar dattawan Najeriya
Sanata Godswill Akpabio a majalisar dattawa. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa gyaran dokar, wanda majalisar ta amince da shi a ranar Alhamis, ya ƙara tsaurara hukunce-hukuncen laifukan titi daban-daban.

Hukuncin wa'azi da talla a mota

A ƙarƙashin sabuwar dokar, duk wanda aka kama yana talla, kasuwanci, ko yin wa'azi a cikin motar sufuri ya aikata laifi. Idan kotu ta same shi da laifi, zai fuskanci tarar ₦50,000.

Sanatocin sun bayyana cewa an kawo wannan sashe ne domin hana shagaltar da direbobi da fasinjoji a cikin motocin sufuri, wanda hakan zai inganta tsaron rayukan matafiya a faɗin ƙasar.

Tarar tuki bayan shan barasa

Baya ga batun wa'azi da talla, ƙudirin ya kuma tsaurara matakai kan direbobin da ke tuƙi bayan sun sha giya ko kwayoyi. An ƙara tara daga ₦5,000 zuwa ₦100,000.

Masu keta wannan doka kuma na iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, ko kuma duka biyun idan har laifin ya tsananta.

Kara karanta wannan

Kotu ta hukunta mutumin da aka kama da laifin ta'addanci

Haka kuma, direbobin da suka ƙi ba da haɗin kai ga jami'an FRSC don yin gwajin numfashi a kan titi za su fuskanci tarar ₦50,000 ko ɗaurin watanni shida.

Tashar mota a Najeriya
Motoci na shirin daukar fasinja a tashar Awala da ke Bauchi. Hoto: Legit
Source: Original

Sauran tarar keta dokokin titi

Haka kuma, gudun da ya wuce kima, wanda a baya tararsa ₦5,000 ce, yanzu ya koma ₦100,000. Tuƙin ganganci ma zai jawo tarar ₦100,000 ko ɗaurin shekaru biyu.

Vanguard ta rahoto cewa sabuwar dokar ta sake nazarin laifuka 52 na titi da kuma tara da ke tattare da su don tabbatar da cewa titunan Najeriya sun zama mafi aminci ga kowa.

Majalisa ta tallafawa daliban Oyo

A wani labarin, mun kawo muku cewa majalisar dattawa ta yaba da da kokarin da hukumomi suka yi wajen ceto daliban da aka sace a Oyo.

Hakan na zuwa ne bayan dakarun sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun shafe lokaci suna farautar 'yan ta'addan da suka sace daliban.

Bayan kwararo yabo ga gwamnati, 'yan majalisar sun tallafawa iyalan dalibai da malaman da zunzurutun kudi har Naira miliyan 50 don rage radadin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng