Dan Gwagwarmaya Ya Tsinci Kansa a Asibiti bayan Yajin Aikin Cin Abinci na Kwana 20

Dan Gwagwarmaya Ya Tsinci Kansa a Asibiti bayan Yajin Aikin Cin Abinci na Kwana 20

  • Wani dan gwagwarmaya a kasar India Sonam Wangchuk ya kwashe kwanaki 20 yana yajin cin abinci
  • Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan sanda su kai shi asibiti saboda tabarbarewar lafiyarsa da ake ganin matsala ce
  • Wangchuk na neman Ministan Ilimi Dharmendra Pradhan ya yi murabus kan zargin tafka kura-kurai a jarabawar shiga karatun likitanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

India - 'Yan sandan birnin Delhi sun dauke fitaccen dan gwagwarmayar a kasar India, Sonam Wangchuk, zuwa asibiti.

Rundunar ta kai shi asibiti ne saboda tabarbarewar lafiyarsa bayan ya shafe kwanaki 20 yana yajin cin abinci.

Dan gwagwarmaya ya kwana a asibiti bayan yajin aikin cin abinci
Dan gwagwarmaya a India, Sonam Wangchuk a asibiti bayan yajin aikin cin abinci. Hoto: Vipin Kumar/Hindustan Times.
Source: Getty Images

Dalilin fara yajin aikin cin abinci

Wangchuk mai shekaru 59 ya fara yajin cin abinci tun ranar 28 ga Yuni domin neman Ministan Ilimi, Dharmendra Pradhan, ya yi murabus kan zargin kura-kurai a jarabawar shiga karatun likitanci, cewar DW.com.

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe ya fara shirin samawa Tinubu kuri'a miliyan 1 a 2027

Daruruwan dalibai sun shiga tare da Wangchuk a dandalin Jantar Mantar da ke New Delhi, yayin da wasu kungiyoyi suka shirya zanga-zangar goyon baya ta intanet.

Mataimakin kwamishinan 'yan sandan Delhi ya ce an kai Wangchuk asibiti bisa umarnin kotu da kuma shawarar kwararrun likitoci saboda lafiyarsa ta kara tabarbarewa.

Ya kara da cewa wasu masu zanga-zanga sun yi kokarin hana jami'an tsaro aiwatar da umarnin, lamarin da ya haifar da dan rikici kafin aka fitar da Wangchuk.

Bidiyon da aka dauka a Jantar Mantar ya nuna yadda aka samu rudani tsakanin magoya bayansa yayin da 'yan sanda suka rufe shi da fararen zanen gado suka fitar da shi.

Tun da farko, babbar kotun Delhi ta umarci likitocin gwamnati su rika duba lafiyar Wangchuk kullum bayan wata kara ta nuna cewa rayuwarsa na cikin hadari.

Kotu ta jaddada cewa rayuwar kowane dan kasa tana da muhimmanci, tare da umartar a ba Wangchuk duk wata kulawar lafiya da za ta taimaka wajen ceton rayuwarsa.

Likitoci yayin da suke duba Sonam Wangchuk
Dan gwagwarmaya daga India, Sonam Wangchuk lokacin da likitoci ke duba shi. Hoto: Arun SANKAR / AFP.
Source: Getty Images

Ayyukan da Sonam Wangchuk ke yi a India

Wangchuk, wanda injiniya ne, ya shahara saboda kirkire-kirkire da ayyukan adana ruwa a yankunan tsaunukan Himalaya da suka taimaka wa al'ummomi, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Yadda Abba Kabir ya ba 'yan APC miliyoyi da filaye sama da 1,500 a Kano

Kafin 'yan sanda su dauke shi, Wangchuk ya ce ko kananan gwagwarmaya sun taba kifar da gwamnatoci a Indiya, yana mai cewa wannan fafutuka ta shafi ilimi ne.

A watan da ya gabata, daliban da suka kai miliyan 2.2 sun sake rubuta jarabawar shiga karatun likitanci bayan an soke ta sakamakon satar takardun jarabawa.

Soke jarabawar da kuma rikicin tantance sakamakon wasu jarabawar sakandare sun jawo fushin matasa, yayin da 'yan adawa suka bayyana goyon bayansu ga Wangchuk da daliban masu zanga-zanga.

An tura yara TikTok gidan yari

An ji cewa wata mai amfani da TikTok a Ghana, Camilla Alhassan, ta gamu da hukuncin ɗaurin shekara guda saboda yaɗa labaran ƙarya a Ghana.

Kotu ta ce hukuncin zai zama darasi ga masu yaɗa ƙarya a kafafen sada zumunta, yayin da lamarin ya sake jawo da muhawara.

Masu gabatar da ƙara sun ce Alhassan ta wallafa zarge-zargen da ba su da hujja, lamarin da ya ƙara tayar da damuwa kan yaɗuwar bayanan ƙarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.