PDP: Kotu za Ta Sanar da Pantami Makomarsa game da Takarar Gwamna a Gombe

PDP: Kotu za Ta Sanar da Pantami Makomarsa game da Takarar Gwamna a Gombe

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta kammala sauraron ƙarar da aka shigar kan zaɓen fitar da gwani na gwamna a jam'iyyar hamayya ta PDP
  • Khamisu Mailantarki na neman kotu ta soke zaɓen fitar da gwanin da ya bai wa Farfesa Isa Pantami tikitin takarar gwamna na jam'iyyar PDP
  • Mai ƙarar ya yi zargin cewa fitaccen malamin ba cikakken ɗan jam'iyyar PDP ba ne lokacin da aka gudanar da zaɓen fitar da gwanin da ya ba shi nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Gombe – Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta kammala sauraron ƙarar da mai neman takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Khamisu Mailantarki, ya shigar gabanta.

Khamisu Mailantarki ya shigar da karar ne yana ƙalubalantar sahihancin zaɓen fitar da gwamnan da jam'iyyar ta gudanar a ranar 26 ga Mayu, 2026

Kara karanta wannan

Kotu ta ci tarar dan takarar gwamna a ADC miliyoyi kan fastocin siyasa a Adamawa

Kotu ta gama sauraron kara kan takarar gwamna a Gombe
Farfesa Isa Ali Pantami, dan takarar gwamna a jihar Gombe Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa zaɓen ne ya fitar da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Isa Pantami, a matsayin ɗan takarar gwamnan PDP domin zaɓen shekarar 2027.

Kotu ta yi magana kan shari'ar Pantami

Daily Post ta wallafa cewa mai shari'a Amina-Aliyu Mohammed ta saurari bayanan lauyoyin ɓangarorin biyu kafin ta sanar da cewa za ta yanke hukunci a wani lokaci da za a sanar da dukkannin masu ruwa da tsaki nan gaba.

Lauyan Mailantarki, Mustapha Ibrahim (SAN), ya shaida wa manema labarai bayan zaman kotun cewa ƙarar na ƙalubalantar halaccin zaɓen fitar da gwanin ne, saboda an ba wanda bai cancanci shiga takarar ba damar yin takara.

Ya ce kotun ta saurari kokensu da hujjojin da suka gabatar mata wanda shi ne ya sanya su kalubalantar fitacceb malamin, Farfesa Isa Ali Pantami.

Bukatar mai neman takara kan Pantami

Mustapha Ibrahim ya ce ficewar ɗaya daga cikin masu ƙarar ba ta shafi shari'ar ba, domin Mailantarki, wanda shi ne babban mai ƙarar, har yanzu yana ci gaba da neman adalci a kotu.

Kara karanta wannan

NDC: Rikici kan zaɓen ƴan takara na ci gaba da rikita jam'iyyar su Kwankwaso

A cewarsa, suna roƙon kotu ta soke sakamakon zaɓen fitar da gwamnan da aka gudanar ranar 26 ga Mayu, 2026 tare da umartar PDP ta sake gudanar da wani sabon zaɓe wanda zai haɗa da 'yan takarar da suka cancanta kaɗai.

Ya kuma yi zargin cewa Isa Ali Pantami ba cikakken ɗan jam'iyyar PDP ba ne lokacin da aka gudanar da zaɓen, don haka bai kamata a bar shi ya shiga takarar ba.

A nasa ɓangaren, lauyan PDP, Kamaldeen Ajibade (SAN), ya tabbatar da cewa akwai shari'o'in zaɓe uku da suka shafi jam'iyyar a gaban kotun.

An fara hango wa Pantami nasara

A wani labarin kun ji cewa malami a jami'ar ABU da ke Zariya a jihar Kaduna, Kabir Danladi Lawanti ya yi nasa hasashen da yake nuna a halin yanzu tauraruwar Isa Ali Pantami tana haskawa.

Ana jiran kotu ta sanar da hukunci kan sharia'arsa Pantami
Taswirar jihar Gombe da ke Arewa maso Gabas Hoto: Legit.ng
Source: Original

Malamin jami’ar mai sharhi a kan al’amuran yau da gobe ya ce akwai abubuwan da za su iya taimakon PDP a jihar Gombe tare da tabbatar da nasarar Farfesa Isa Ali Pantami a zaben gwamna mai zuwa.

Malamin jami’ar wanda shi kan shi ‘dan asalin jihar Gombe ne kuma wanda ya saba sharhi a kan al’umuran yau da gobe ya jero hujjojinsa, inda ya ce kasancewarsa malamin addinin Musulunci zai taimaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng