'Yan Sanda Sun Fara Tone Tone kan Samun Gawar Budurwa a Gidan Ministan Tinubu

'Yan Sanda Sun Fara Tone Tone kan Samun Gawar Budurwa a Gidan Ministan Tinubu

  • Rundunar 'yan sanda ta jihar Ebonyi ta bukaci a gudanar da binciken gawa bayan an sami gawar Mary Habila, mai shekaru 26, a gidan Ministan Ayyuka, David Umahi
  • Binciken farko ya nuna cewa Habila tana cikin tawagar ma'aikatan lafiya da suka raka Umahi zuwa gidansa, inda ta rasu a wani daki da ke cikin gidan ministan
  • Iyalan Mary Habila sun ki amincewa da gudanar da binciken gawar, amma 'yan sanda sun dage cewa dole ne a yi shi domin gano hakikanin musabbabin mutuwarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta fitar da sanarwa tana neman a gudanar da binciken gawa bayan an samu gawar wata ma'aikaciyar jinya, Mary Habila, mai shekaru 26, a gidan Ministan Ayyuka, David Umahi, da ke garin Uburu.

Kara karanta wannan

An taso ministan Tinubu a gaba ya yi murabus bayan mutuwar budurwa a gidansa

Kakakin rundunar, SP Joshua Ukandu, ya bayyana a wata sanarwa ranar Laraba cewa an sanar da 'yan sanda game da lamarin ne a ranar 27 ga Yunin 2026.

David Umahi da Mary Habila
Ministan ayyuka, David Umahi a hagu da Mary Habila a dama. Hoto: @Pharmacio001, @realdaveumahi
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa ya ce jami'an 'yan sanda sun gaggauta kai dauki, kuma bayan an garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na David Umahi da ke Uburu, likitoci sun tabbatar da cewa ta riga ta rasu kafin a kawo ta.

Budurwa ta raka minista Umahi

Binciken farko da 'yan sanda suka gudanar ya nuna cewa Mary Habila da wata abokiyar aikinta mai suna Anita Baaki suna cikin tawagar ma'aikatan lafiya da ke kula da lafiyar Minista Umahi.

Rahoton Vanguard ya nuna cewa sun raka shi zuwa garinsa na Uburu, inda Mary Habila ta rasu a wani daki da ke cikin gidan ministan.

Matakin da 'yan sanda suka dauka

Bayan an sanar da kwamishinan 'yan sanda halin da ake ciki, ya bayar da umarnin a mika shari'ar ga Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na Jiha (SCID) domin gudanar da cikakken bincike.

Tun daga lokacin, jami'an bincike suka ziyarci wurin da lamarin ya faru tare da tattara bayanai daga mutanen da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Mutane sun yi kukan kura sun kama dan bindiga a jihar Kano

Maganar bincike gawar budurwar

Duk da yake cewa rundunar ta shirya dauko kwararren likitan binciken gawa domin gudanar da aikin, iyalan Mary Habila sun ki amincewa da hakan.

Sai dai rundunar ta bayyana cewa ba za a yi rufa-rufa a shari'ar ba tare da gudanar da binciken gawar ba, domin gano hakikanin musabbabin mutuwarta.

'Yan sanda sun ce suna jiran iyalan mamaciyar ko wakilinsu su halarci lokacin da za a gudanar da binciken gawar, suna jaddada cewa kasancewarsu zai taimaka wajen tabbatar da adalci da gaskiya.

Sufeton 'yan sandan Najeriya
Shugaban 'yan sanda na kasa, Tunji Disu. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Rundunar ta kuma yi alkawarin gudanar da bincike cikin adalci da gaskiya, tare da ci gaba da sanar da jama'a yadda binciken ke gudana.

Hadari ya kashe mutane a Kogi

A wani rahoton, mun kawo muku cewa hadarin motar gas ya jawo asarar rayuka akalla shida a kan wata babbar hanya a Kogi.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Abuja-Lokoja da ke jihar Kogi a kusa da shingen sojoji.

Legit Hausa ta samu rahoton da ya tabbatar da cewa matukin motar da abokin aikinsa na cikin mutanen da suka kone kurmus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng