Tsohon Gwamnan da Ya Sha Bakar Wahala a Hannun APC Ya Fito Kare Shugaba Tinubu
- Tsohon gwamnan jihar Katsina, Barista Ibrahim Dhehu Shema ya kare matakan tattalin arziki na shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
- Shema ya kaddamar da kungiyar kamfe da ya radawa suna, Tinubu-Dikko Again 2027 a fadin kananan hukumomin Katsina
- Kungiyar za ta yi aikin wayar da kan mata da matasa a dukkan kananan hukumomi 34 gabanin babban zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema, ya kaddamar da wata kungiyar wayar da kan jama’a ta APC) domin karfafa goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Dikko Umar Radda kafin zaben 2027.
Shema ya kaddamar da kungiyar mai suna Tinubu-Dikko Again 2027 ne yayin bude cibiyar mata da matasa ta kungiyar da ke kan titin Daura kusa da sansanin Alhazai a Katsina.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa kungiyar za ta kasance wata kafa ta wayar da kan jama'a a matakin kasa, wacce za ta hada mata da matasa tare da kara karfafa jam'iyyar APC, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Shema ya kare manufofin Tinubu, Radda
Tsohon gwamnan ya bukaci mambobin APC su kara himma wajen tuntubar jama'a tare da kare manufofin gwamnatin Bola Tinubu da Radda.
Ya ce duk da cewa wasu daga cikin matakan tattalin arzikin da gwamnatin ta dauka sun jawo wa mutane wahala, amma sun zama dole domin magance matsalolin da suka dade suna addabar Najeriya.
Shema ya ce:
"Wasu matakan da Bola Ahmed Tinubu ya dauka a matsayin shugaban kasa da kuma wadanda Gwamna Dikko Umar Radda ya dauka suna iya zama masu wahala ga 'yan Najeriya."
"Amma wadannan matakai sun zama dole domin gyara matsalolin tattalin arziki, tsaro da walwalar al'umma."
Shema ya bayyana cewa wannan kungiyar za ta kafa rassa a dukkan kananan hukumomi 34 na jihar, gundumomi da kuma rumfunan zabe domin wayar da kan jama'a kan manufofin Tinubu da Dikko Radda, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan
Kwankwason APC ya ari bakin 'yan Arewa, ya yi magana kan tikitin Tinubu da Shettima a 2027
Gwamna Radda ya nuna kwarin gwiwa
Gwamna Dikko Radda, wanda ya kaddamar da kwamitocin kungiyar daga matakin jiha zuwa rumfunan zabe, ya ce kungiyar za ta taka muhimmiyar rawa wajen hada kan mata da matasa kafin zaben 2027.
Radda ya ce:
"Ba ni da wata shakka ko fargaba game da damar da muke da ita na samun nasara a zabe mai zuwa."
Ya kara da cewa kwarin gwiwarsa ya samo asali ne daga taimakon Allah, goyon bayan shugabannin jam'iyya da kuma amincewar al'ummar jihar da gwamnatinsa.

Source: Facebook
An fara juyawa Tinubu baya kafin 2027
A wani labarin, kun ji cewa wani jigon jam'iyyar APC a jihar Neja, Jonathan Vatsa, ya soki matakin Shugaban kasa, Bola Tinubu na daukar Kashim Shettima a matsayin abokin takara a 2027.
Vatsa ya ce sake zaɓar Mataimakin Shugaban Ƙasa , Kashim Shettima , a matsayin abokin takararsa zai jawo masa matsala ga Shugaba Tinubu da jam'iyyar APC.
Ya ce maimaita tsarin da aka yi a zaɓen 2023 cin fuska ne ga al'ummar Kiristoci a Najeriya, kuma hakan ya nuna rashin kula da damuwarsu
Asali: Legit.ng
