Tsohon Minista Ya Amsa Kiran Allah, Ya Mutu Yana Shekara 87
- Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha a Najeriya, Farfesa Turner Timinipre Isoun ya koma ga Mahaliccinsa yana da shekaru 87 a duniya
- Iyalan mamacin sun sanar da cewa ya rasu ne a tsakiyar mako, kuma za a bayyana shirye-shiryen jana'iza idan an kammala shirye-shirye
- Marigayin yana daga cikin hazikan yan Najeriya da suka samu tallafin karatun gwamnati daga digirin farko har zuwa digirin digirgir a kasar waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bayelsa- Iyalan tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Farfesa Turner Timinipre Isoun, sun sanar da rasuwarsa yana da shekara 87 a duniya.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da kakakin iyalan Isoun a garin Odi da ke jihar Bayelsa, Mista Diseye Timinipre Isoun ya fitar, ya ce shugaban iyalan, Farfesa Turner Timinipre Isoun, ya rasu ne a ranar Laraba 15 ga watan Yuli, 2026.
The Nation ta wallafa cewa sanarwar ta bayyana cewa an haifi marigayin ne a ranar 2 ga Satumban shekarar 1938. ga iyayensa, Mark Ebidi Isoun da Dali Amgbapu Isoun.
Ana shirin jana'izar tsohon minista
Jaridar The Sun ta kawo labarin cewa Iyalan sun ce za su sanar da jama'a shirye-shiryen jana'izar marigayin a lokacin da ya dace a nan gaba.

Source: Original
Marigayi Farfesa Turner Isoun ya yi fice a harkar ilimi tun yana matashi, inda ya samu tallafin karatu daga gwamnatin tarayya domin ci gaba da karatu a Jami'ar Michigan State da ke kasar Amurka.
A jami'ar, ya samu digirin farko na BSc a shekarar 1963, sannan ya kammala karatun digiri a kan lafiyar dabbobi (DVM) a shekarar 1965.
Yadda tsohon minista ya zurfafa karatu
Bayan haka, ya ci gaba da zurfafa karatu har ya samu PhD a shekarar 1970. Farfesa Isoun ya kasance daya daga cikin fitattun masana da suka taka rawa wajen bunkasa harkokin kimiyya da fasaha a Najeriya, lamarin da ya kai ga nada shi Ministan Kimiyya da Fasaha a gwamnatin tarayya.
Rasuwarsa ta kawo karshen rayuwar wani fitaccen masani da ya bayar da gudunmawa wajen ci gaban ilimi, binciken kimiyya da kuma hidimar kasa.
Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, iyalansa ba su bayyana musabbabin rasuwarsa ba, sai dai sun tabbatar da cewa za su sanar da cikakken shirin jana'izarsa a nan gaba.
'Dan majalisa ya rasu a Bauchi
A baya, mun kawo labarin cewa an yi rashi na daya daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Sakwa a majalisar dokokin jihar Bauchi, Wanzam Mohammed Zaki, ya yi bankwana da duniya.
Shugaban majalisar dokoki da Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, sun aika da sakon ta'aziyyarsu kan rashin jagora wanda ya rasu bayan ya yi fama da gajeriya rashin lafiya da ta yi ajalinsa.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana marigayin a matsayin dan majalisa jajirtacce, shugaba mai tawali'u, kuma mai yi wa jama'a hidima, sadaukarwa wanda ya tsaya wajen inganta rayuwar jama'a.
Asali: Legit.ng

