PFIPC: Gbajabiamila Ya Gagara Hakuri, Ya Maka Adeyemi a Kotu, Ya Bukaci Diyya

PFIPC: Gbajabiamila Ya Gagara Hakuri, Ya Maka Adeyemi a Kotu, Ya Bukaci Diyya

  • Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya shiga kotu kan alakanta shi da hukumar bogi
  • Gbajabiamila ya shigar da kara a kotun babban birnin tarayya kan Adeniyi Adeyemi bisa zargin bata masa suna
  • Haka kuma ya bukaci kotu ta umarci Adeyemi ya janye kalaman da ake zargi da bata suna tare da neman afuwa a jaridu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya maka Adeniyi Adeyemi a kotu.

Gbajabiamila ya shigar da kara a babbar kotun babban birnin tarayya kan shugaban hukumar bogi ta PFIPC.

Gbajabiamila ya maka Adeyemi a kotu
Femi Gbajabiamila da shugaban hukumar bogi, Adeniyi Adeyemi. Hoto: Femi Gbajabiamila, Bayo Onanuga.
Source: Twitter

PFIPC: Gbajabiamila ya shigar da Adeyemi kara

A cikin karar da aka shigar a kotu, Gbajabiamila yana neman a ba shi diyyar Naira biliyan 10 a matsayin diyya ta gaba daya, cewar TheCable

Kara karanta wannan

Bayan umarnin kotu, an kama shugaban hukumar bogi da ake ta cece kuce a kanta a Najeriya

Sannan ya bukaci a kara masa Naira biliyan 5 a matsayin karin diyya saboda tsanantar lamarin.

Har ila yau, ya bukaci kotu ta umurci Adeyemi ya biya kudin shari'ar da suka kai Naira miliyan 200, saboda yadda aka tafiyar da wannan shari'a.

Bugu da kari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ya bukaci kotu ta umurci Adeyemi ya wallafa cikakken janye kalaman da ake zargi da bata suna tare da neman afuwa.

An shigar da shugaban hukumar bogi na PFIPC kotu
Shugaban hukumar bogi ta PFIPC da ake zargi da badakala. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Bukatar Gbajabiamila a kotu kan Adeyemi

Gbajabiamila ya ce ana so a wallafa wannan janye kalamai da neman afuwar a cikin manyan jaridun kasa guda biyar domin gyara barnar da aka yi wa sunansa.

Rahoton ya bayyana cewa karar ta samo asali ne daga zargin bata suna da Gbajabiamila ya ce an yi masa daga bakin Adeniyi Adeyemi, babban daraktan PFIPC.

Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, ba a bayyana cikakken bayanin zargin bata sunan da ya haddasa shigar da karar ba.

Ana sa ran za a samu karin bayani daga kotu ko bangarorin da abin ya shafa yayin da shari'ar ke ci gaba a kwanaki masu zuwa.

Kara karanta wannan

Adeyemi: 'Yadda na samo aron N400m wajen kafa hukumar bogi

Maimakon ya janye zarge-zargen, Gbajabiamila ya ce Adeyemi ya yi hira da Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, wanda aka wallafa a Instagram.

A hirar, ya amince cewa bai taɓa haɗuwa da mai ƙarar ba, kuma duk wata mu'amala da ya yi ikirarin yi ta kasance ne ta hannun marigayi Tanimola.

Har ila yau, Adeyemi ya sake ba da wata hira a gidajen jaridu da aka watsa a ranar 13 ga Yuli, wanda Seun Okinbaloye ya gabatar.

Gbajabiamila na roƙon kotu ta ayyana cewa kalaman da Adeyemi ya furta kuma aka wallafa ƙarya ne, na mugunta kuma bata suna ne.

Yadda Adeyemi ya tattauna da Gbajabiamila

An ji cewa Adeniyi Adeyemi mai ikirarin shugabantar PFIPC ya ce bai taɓa haɗuwa da Femi Gbajabiamila ido da ido ba kafin ko bayan ikirarin naɗa shi.

Ya bayyana cewa duk tattaunawarsa da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa ta gudana ne ta hannun marigayi Dolapo Tanimola.

Adeyemi ya sake roƙon shugaban ƙasa ya kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar lamarin hukumar PFIPC da ake zargi da badakal mafi girma a kasar

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.