'Tana da Kishin Addini': An Shiga Jimami bayan Rasuwar Mahaifiyar Amaechi
- Tsohon ministan sufuri kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na ADC, Rotimi Amaechi ya tafka babban rashi
- An tabbatar da cewa Amaechi ya rasa mahaifiyarsa mai suna Mary Amaechi wacce ta rasu tana da shekara 89.
- Iyalanta sun ce Mary Amaechi ta kasance shugabar mata a al'umma, mai kishin addinin Kirista
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt - Tsohon ministan sufuri kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a zaɓen 2027, Rotimi Amaechi ya rasa mahaifiyarsa.
Majiyoyi sun ce Rotimi Amaechi ya rasa mahaifiyarsa, Mary Amaechi, wacce ta rasu tana da shekara 89.

Source: Twitter
Iyalan marigayiyar sun sanar da rasuwarta cikin wata sanarwa da Ofishin Yaɗa Labaran Rotimi Amaechi ya fitar, cewar Vanguard.
Yaushe mariyayiyar ta bar duniya?
Sun ce Mary Amaechi ta rasu cikin lumana a ranar Alhamis 16 ga watan Yulin shekarar 2026 bayan fama da jinya.
Sanarwar ta bayyana marigayiyar a matsayin ƙwararriyar Kirista kuma shugabar al'umma mai daraja, wacce ta sadaukar da rayuwarta wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da hidima ga jama'a.
Iyalan sun ce Mary Amaechi ta kasance ginshiƙin iyali, tana riƙe danginta cikin ƙauna, zaman lafiya da haɗin kai.
Haka kuma ta kasance shugabar mata da shugabar Kirista mai cikakken imani da Ubangiji, kamar yadda Punch ta ce.
Sun ƙara da cewa marigayiyar ta samu girmamawa sosai a cikin al'ummarta da ma wajen sauran jama'a saboda tausayinta, karamcinta da kuma goyon bayan da take bai wa mutane.

Source: Facebook
Alherin da marigayiyar ta bari a baya
A cewar sanarwar, za a ci gaba da tuna Mary Amaechi saboda kyakkyawar mu'amalarta, alherinta da kuma yadda ta kasance mai taimaka wa na kusa da na nesa.
Iyalan sun kuma bayyana godiyarsu ga dimbin mutane da suka nuna alhini tare da aika saƙonnin ta'aziyya bayan rasuwar marigayiyar, sun ce wannan ƙauna ta ƙarfafa musu gwiwa a wannan lokaci mai wahala.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a sanar da cikakkun bayanan shirye-shiryen jana'izar Mary Amaechi nan gaba.
Iyalan sun roƙi abokai, magoya baya da masu fatan alheri su ci gaba da yi musu addu'a domin samun damar yin hakurin rashin.
Rotimi Amaechi ya taɓa zama gwamnan Rivers sannan daga baya ya yi aiki a matsayin ministan sufuri.
Yanzu shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC domin babban zaɓen shekarar 2027 tsakanin Atiku, Tinubu, Peter Obi da sauran yan takara.
Kungiya ta bukaci sauya Amaechi a mataimakin Atiku
Kun ji cewa wata kungiyar siyasa ta bukaci Atiku Abubakar ya sauya tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin mataimakinsa.
Kungiyar ta ce Amaechi ba shi da karfin siyasa da zai kara wa ADC damar samun kuri'u a babban zaben 2027 mai zuwa.
SPPAF ta bukaci dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC ya zabi mataimaki mai farin jini da karfin goyon bayan jama'a.
Asali: Legit.ng

