Sule Lamido Ya Faɗi Abin Mamaki da Abacha Ya Yi Masa bayan Shaƙuwar da Suka Yi

Sule Lamido Ya Faɗi Abin Mamaki da Abacha Ya Yi Masa bayan Shaƙuwar da Suka Yi

  • Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana yadda ya ta kaya tsakaninsa da marigayi Janar Sani Abacha
  • Ya ce Abacha ya sha alwashin mika mulki ga farar hula, amma daga baya ya fasa, wanda hakan ya janyo sabani tsakaninsu
  • Bayan kin yarda da tsarin mulkin Abacha, shi da Abubakar Rimi suka fuskanci tsangwama, har aka kama su cikin dare

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi magana kan alakarsa da marigayi Janar Sani Abacha.

Sule Lamido bayyana yadda ya sauya daga abokin marigayi Sani Abacha zuwa ɗaya daga cikin fursunonin da ke daur.

Lamido ya fadi abin da Abacha ya yi masa
Sule Lamido ya koka kan cafke shi da Abacha ya yi. Hoto: Sule Lamido.
Asali: Twitter

Sule Lamido ya fadi yadda suka yi da Abacha

Wannan bayani yana cikin shafi na takwas na littafinsa mai suna “Being True To Myself” da aka kaddamar a ranar 13 ga Mayu, 2025, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A shafin da ya kira “Shekarun Abacha,” Lamido ya ce sun fara mu’amala da Abacha tun 1980 a zamanin jamhuriya ta biyu a Najeriya.

Sule Lamido ya ce lokacin yana majalisar wakilai ne, yayin da Abacha ke sojan da ke yawan kai ziyara wajen Sarki Adamu a Lagos.

Ya ce:

“Muna tare cikin zumunci da dariya, na taba gaya wa Abacha cewa yana kama da wanda zai yi juyin mulki"

Ya ce Abacha ya yi watsi da maganar, yana cewa ba shi da sha’awar shiga siyasa, kamar yadda Sule Lamido ya bayyana a littafinsa.

Bayan Abacha ya hau mulki, an naɗa shi a cikin wakilan taron tsarin mulki, wanda ya dawo daga Saudiyya don halarta.

Sule ya nemi karin bayani daga Abacha kai tsaye, inda ya tabbatar masa cewa zai mika mulki bayan taron.

Abacha ya ce:

“Ina so in mika mulki, ku ba mu taro nagari don in mika mulki cikin kwanciyar hankali.”

Lamido ya fadi yadda Abacha ya cafke shi
Sule Lamido ya tuno abotarsa da Abacha tun farko. Hoto: Sule Lamido.
Asali: Facebook

Yadda Sule Lamido ya fuskanci Abacha ido da ido

'Dan siyasar ya daɗe yana fatan haka, amma daga baya ya fara zargin cewa Abacha ba ya da niyyar barin mulki.

A lokacin taron, Sule Lamido ya fuskanci Abacha yana cewa idan ya sauya ra’ayi, ba zai mara masa baya ba.

“Na fada masa a fili, idan ya fasa mika mulki, ba zan goya masa baya ba. Kuma ma zan yi adawa."

- Cewar Sule Lamido

Abacha ya yi dariya, suka rabu a haka amma daga nan Lamido ya fahimci sabani ya fara shiga tsakaninsu.

Alhaji Sule Lamido ya ce an kafa jam’iyyu da dama, inda nasu ba a yarda da su ba, amma na kawayen Abacha sun samu rajista.

Saboda haka, Lamido da wasu suka fice daga tsarin mulkin, suka aika da takarda ga gwamnati suna sanar da matsayinsu.

Ya ce:

“A daren taronmu, aka kama ni da Abubakar Rimi ashe ami’an DSS suna biye da mu tun farko.

“Da na isa gida misalin karfe 10:30 na dare, suka zo suka kama ni."

Duk da wannan wahala, Sule Lamido ya bayyana sirrin yadda gwamnatin Abacha ke aiki da kuma ƙarfin gwiwar da ya nuna.

Sule Lamido ya fadi yadda suka yi da IBB

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya fadi yadda ya yi jarumta yayin tattaunawarsu da Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Tsohon gwamnan ya ce ido da ido ya kalli IBB ya fada masa cewa ya yi murabus kan soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993.

Lamido ya ce IBB ya yi mamakin yadda ya yi tsaurin ido har ya iya fada masa ya yi murabus daga mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.