Babban Jigon APC a Arewa Ya Yi Magana kan Barin Jam'iyyar bayan Tinubu Ya Zabi Shettima

Babban Jigon APC a Arewa Ya Yi Magana kan Barin Jam'iyyar bayan Tinubu Ya Zabi Shettima

  • Rt. Hon. Yakubu Dogara ya ce rahotannin da ke cewa zai fice daga APC kan tikitin Musulmi da Musulmi na 2027 ƙarya ne tsagwaronta
  • Tsohon kakakin majalisar wakilan ya tabbatar da cewa yana nan daram a APC kuma zai yi aiki domin nasarar Bola Tinubu a 2027
  • Mai magana da yawun Dogara ya zargi masu haddasa rikici da ƙirƙirar jita-jitar domin raba kan APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara, ya yi martani kan rahotannin da suka bazu cewa yana shirin ficewa daga jam'iyyar APC.

Wasu rahotanni sun ce Dogara zai bar APC saboda tikitin Musulmi da Musulmi da ake hasashen jam’iyyar za ta yi amfani da shi a babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Mataimakin shugaban APC da wasu manyan ƙusoshi sun fice daga jam'iyyar

Yakubu Dogara ya ce ba zai bar jam'iyyar APC ba kuma yana tare da Bola Tinubu a 2027
Tsohon kakakin majalisa, Yakubu Dogara (hagu) da Shugaba Bola Ahmed Tinubu (dama). Hoto: Sulaiman Abdullahi/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Dogara ya yi watsi da jita-jitar barin APC

Dogara ya bayyana rahotannin a matsayin ƙarya marar tushe, yana mai cewa wasu masu neman haddasa rikici ne suka ƙirƙire su domin yaudarar jama'a da kuma haifar da rashin jituwa a cikin jam’iyyar APC, in ji rahoton The Nation.

Ya kuma tabbatar da cewa har yanzu shi cikakken ɗan APC ne mai biyayya ga manufofin jam’iyyar.

A wata sanarwa da kakakinsa, Dr. Dominic Alancha, ya fitar a Abuja ranar Talata, an bayyana cewa tsohon kakakin majalisar ba shi da niyyar barin APC, kuma bai taɓa bayyana hakan a wani lokaci ba.

Sanarwar ta ce rahotannin da ke cewa Dogara zai fice daga jam’iyyar saboda tikitin Musulmi da Musulmi ƙarya ce da aka ƙirƙira domin tayar da kura a siyasa.

"Muna magana da babbar murya cewa waɗannan rahotanni ƙarya ne kuma ba su da wani tushe. Rt. Hon. Yakubu Dogara har yanzu cikakken mamba ne na APC, kuma bai yi murabus daga jam’iyyar ba ko kuma nuna niyyar yin hakan," in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta fara daukar sababbin ma'aikata, matasa 3050 za su samu aiki

Tsohon kakakin ya goyi bayan Tinubu

Ta kuma zargi wasu masu son raba kan APC da ƙirƙirar irin waɗannan rahotanni domin haifar da rashin haɗin kai tsakanin shugabanni da mambobin jam’iyyar yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

Sanarwar ta ƙara da cewa Dogara na ci gaba da aiki tare da shugabannin APC a matakai daban-daban domin ƙarfafa jam’iyyar da kuma tabbatar da nasararta a zaɓen 2027, in ji rahoton This Day.

Ta bayyana cewa tsohon kakakin majalisar ya himmatu wajen ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake samun nasara a wa’adinsa na biyu, tare da ci gaba da tallafa wa manufofin gwamnati da nufin bunƙasa ƙasa.

Yakubu Dogara ya ce wasu 'yan hana ruwa gudu ne ke yada cewa yana shirin barin jam'iyyar APC
Tsohon kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara yana jawabi a wani taro. Hoto: Rt. Hon. Yakubu Dogara
Source: Facebook

Tinubu zai ba da gudunmawa a ci gaban APC

A cewar Alancha, Dogara na da cikakken ƙuduri na haɗa kan jam’iyyar da ƙarfafa dimokuraɗiyya, yana mai cewa zai ci gaba da ba da gudunmawa wajen tabbatar da ci gaban APC da Najeriya baki ɗaya.

Sanarwar ta kuma buƙaci jama'a da magoya bayan jam’iyyar su yi watsi da duk wata jita-jita da ba ta fito daga sahihan hanyoyi ba, tana mai jaddada cewa Dogara ya mayar da hankali ne kan haɗin kan jam’iyya, inganta shugabanci nagari da kuma tabbatar da nasarar APC a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Rashin sani: Shaguben da sanatan Amurka ya yi ga Iran kwana 5 kafin ya mutu

Dogara ya magantu kan zaben 2027

Tun da fari, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya yi magana kan rade-radin cewa zai maye gurbin mataimakin shugaban kasa a zaben 2027 a APC.

Dogara ya ce ya kamata batutuwan rabon madafun iko da daidaiton addini su ta’allaka kan adalci da gaskiya, ba tsoro ko matsin lambar siyasa ba.

Ya bayyana cewa ana tattaunawa kan yiwuwar canza mataimakin shugaban kasa, amma duk shawarar da aka dauka dole ta kasance mai hada kan ‘yan kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com