Kwankwaso Ya Bukaci Gwamnati Ta Aiwatar da Kidayar Jama'a, Ya Fadi Amfanin Hakan

Kwankwaso Ya Bukaci Gwamnati Ta Aiwatar da Kidayar Jama'a, Ya Fadi Amfanin Hakan

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya bukaci gwamnatin tarayya ta gudanar da sahihiyar kidayar jama'a da gidaje ba tare da wani karin jinkiri ba
  • Sanata Kwankwaso ya ce Najeriya ta shafe shekara 20 ba tare da gudanar da sabon kidayar jama'a ba tun bayan wanda aka yi a 2006
  • Tsohon gwamnan ya jaddada cewa amfani da fasaha da tabbatar da gaskiya zai kara ingancin sakamakon kidayar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga gwamnatin tarayya kan kidayar jama'a.

Kwankwaso ya bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta gudanar da sahihiyar kidayar jama'a da gidaje cikin gaskiya da rikon amana tare da amfani da fasahar zamani.

Kwankwaso ya bukaci a yi kidayar jama'a
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taro Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso, wanda shi ne mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, a zaben 2027, ya bayyana hakan ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, 11 ga watan Yulin 2026 domin bikin ranar yawan jama'a ta duniya ta shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Sarkin Zazzau ya ba da shawara kan gudanar da sahihin zabe a Najeriya

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP ya nuna damuwa cewa Najeriya ba ta gudanar da kidayar jama'a ta kasa ba tsawon shekaru 20, yana mai tunatar da cewa an gudanar da kidayar ta karshe ne a shekarar 2006.

Kwankwaso ya nuna illar tsofaffin alkaluma

A cewarsa, ci gaba da amfani da tsofaffin alkaluman yawan jama'a yana kawo cikas ga tsare-tsare da yanke hukunci a muhimman bangarorin tattalin arziki da gudanar da gwamnati.

Ya ce samun sahihan alkaluman yawan jama'a na da matukar muhimmanci wajen kyakkyawan shugabanci, tabbatar da tsaro, gina ababen more rayuwa, inganta harkokin lafiya, tsara ilimi, samar da ayyukan yi da kuma raba albarkatu cikin adalci.

"Abin damuwa ne matuka cewa kasarmu ba ta gudanar da kidayar jama'a da gidaje ba tsawon shekaru 20. Kidayar ta karshe da aka yi a shekarar 2006 ta sa har yanzu muna amfani da tsofaffin alkaluma wajen yanke muhimman shawarwari kan ilimi, lafiya, tsaro, ababen more rayuwa, ayyukan yi da rabon albarkatu."
"Wannan gibin bayanai yana kawo cikas ga ingantaccen tsari da ci gaban kasa cikin adalci. Sahihai kuma sababbin alkaluman yawan jama'a su ne tubalin kyakkyawan shugabanci, tsaron kasa, ci gaba mai dorewa da bunkasar da ta shafi kowa."

Kara karanta wannan

'Kar mu ji, kar mu gani': Atiku ya gargadi gwamnati game da Obi, El Rufa'i

"Ba za mu iya ci gaba da tsara makomar sama da mutane miliyan 200 da alkaluman da aka tattara shekaru 20 da suka gabata ba."

- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Ya bukaci gwamnati ta fifita kidayar jama'a

Kwankwaso ya yi gargadin cewa rashin sababbin bayanan yawan jama'a ya haifar da gibi da ke kawo nakasu ga kokarin ci gaban kasa da kuma tsara manufofi bisa sahihan bayanai.

Ya bayyana cewa ingantattun alkaluman yawan jama'a na zamani su ne ginshikin kyakkyawan shugabanci, tsaron kasa, ci gaba mai dorewa da kuma bunkasar tattalin arziki da ta hada da kowa.

Kwankwaso ya bukaci gwamnati ta yi kidayar jama'a
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Tsohon gwamnan ya jaddada cewa bai dace Najeriya ta ci gaba da tsara makomar al'ummarta mai karuwar yawa bisa alkaluman da aka tattara shekaru 20 da suka gabata ba.

Saboda haka, ya bukaci gwamnatin tarayya ta ba da fifiko ga gudanar da sabon kidayar jama'a da gidaje, yana mai cewa dole ne a gudanar da aikin cikin gaskiya, rikon amana da amfani da fasahar zamani domin tabbatar da sahihancin sakamakon da kuma karfafa amincewar jama'a.

Kwankwaso ya yi wa Ali Modu Sheriff martani

Kara karanta wannan

An kashe bakin tsanya, Kudan da aka 'nadi muryarsa' ya gana da El Rufa'i da ke hannun ICPC

A wani labarin kuma, kun ji cewa madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi martani ga Ali Modu Sheriff.

A cewar Kwankwaso, Ali Modu Sheriff ya yi kuskure da ya yi ikirarin cewa Peter Obi ba zai iya samun gagarumin goyon baya daga al'ummar Arewacin Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng