Lokaci Ya Fara Ƙurewa, Tinubu Ya Sanya Wa'adin da Kowane Dan Najeriya Zai Mallaki NIN
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumar NIMC ta tabbatar kowane ɗan Najeriya ya yi rijistar NIN kafin ƙarshen 2026
- Shugabar NIMC ta kasa, Abisoye Coker-Odusote ta ce tsarin rijistar lambar zama dan kasa ya haramta mallakar NIN guda biyu
- Ta bayyana cewa kammala yi wa kowane dan Najeriya rijistar NIN zai ba da damar sanin jimullar adadin mutanen da kasar ke da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Kasa (NIMC) da ta tabbatar da cewa an yi wa kowane ɗan Najeriya rajistar NIN kafin ƙarshen shekarar 2026.
Umarnin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin tarayya na gina cikakken tsarin shaidar ɗan ƙasa domin inganta shugabanci, tsare-tsare da kuma isar da ayyukan gwamnati.

Source: Twitter
Babbar Darakta kuma Shugabar NIMC, Abisoye Coker-Odusote, ce ta bayyana hakan yayin wata hira da ta yi a shirin Sunday Politics na tashar Channels TV.
Ta ce:
"Shugaban kasa ya ba mu wa'adin zuwa ƙarshen wannan shekara domin tabbatar da cewa mun yi wa kowane ɗan Najeriya rajistar NIN."
NIMC ta haɗa gwiwa da Bankin Duniya
Coker-Odusote ta bayyana cewa NIMC na aiki tare da wasu abokan hulɗa ƙarƙashin shirin Identification for Development (ID4D) na Bankin Duniya domin hanzarta rajistar jama'a a faɗin ƙasar.
A cewarta:
"Mun haɗa kai da abokan hulɗa ta hanyar shirin ID4D na Bankin Duniya. Mun ba wasu kamfanoni masu zaman kansu damar yi mana rajistar 'yan ƙasa domin faɗaɗa aikin."
Ta jaddada cewa Lambar Shaidar Ɗan Kasa (NIN) na musamman ce ga kowane mutum, kuma mutum ba zai samu rajista fiye da ɗaya ba.
Za a san hakikanin yawan 'yan Najeriya
Shugabar NIMC ta ce har yanzu ba a san ainihin yawan al'ummar Najeriya ba, domin akwai mabambantan hasashe tsakanin mutum miliyan 200 zuwa miliyan 250.
Ta ce:
"Ana hasashen muna da mutum miliyan 200. Idan muka kammala rajistar kowa, za mu san hakikanin adadin al'ummar Najeriya. Wasu na cewa mutum miliyan 230 ne, wasu kuma suna cewa miliyan 250."
Ta ƙara da cewa samun cikakken bayanan shaidar jama'a yana da matuƙar muhimmanci wajen tsara manufofi da gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.

Source: Twitter
NIMC ta yi bayani kan mqallakar NIN 2
Da aka tambaye ta ko mutum zai iya yin rajista da sunaye daban-daban ko a wurare daban-daban domin samun NIN fiye da ɗaya, Coker-Odusote ta ce tsarin tantance shaidar yatsu na NIMC ba ya ba da damar hakan.
Ta ce tsohon tsarin na iya karɓar rajista sau biyu kafin ya gano kuskuren daga baya, amma sabon tsarin na gano hakan kai tsaye.
Tinubu ya yi fatali da kudirori 2
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya ƙi amincewa da kudurori biyu da Majalisar Tarayya ta amince da su saboda kura-kurai da suka saɓa wa kundin mulki.
An sanar da Majalisar Dattawa matakin shugaban ƙasar ne ta wasiƙu guda biyu da shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya karanta a zaman sanatoci na makon jiya.
Tinubu ya ce bayan an yi gyaran da ya dace, zai iya sanya hannu domin kudurorin su zama doka, amma a yanzu ba zai iya rattaba hannun ba.
Asali: Legit.ng


