Sule Lamido Ya Yi wa Pantami Shagube kan Kiran PDP 'Al Kafira' a Shekarun Baya
- Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya karbi bakuncin dan .takarar gwamnan Gombe a jam'iyyar PDP
- Jigon PDP, Sule Lamido ya gana da Farfesa Isa Ali Pantami da wasu ƴan takara daga Bauchi, Yobe, Kano da Jigawa
- Tsohon gwamnan ya tuna yadda Isa Ali Pantami ya taɓa kiran PDP da "jam'iyyar kafirai," yana mai sukar sauyin matsayinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dutse, Jigawa - Siyasar gabanin zaɓen 2027 ta sake ɗaukar sabon salo bayan tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya yi wa Isa Ali Pantami shagube.
Sule Lamido ya yi taba tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami kan sukar PDP a baya.

Source: Facebook
Ɗan tsohon gwamnan Jigawa, Mustapha Sule Lamido ya tabbatar da cewa mahaifinsa ya hana da Pantami a Facebook.
Sule Lamido ya karbi bakuncin Pantami
Lamido ya yi wannan bayani ne lokacin da ya karɓi baƙuncin wasu 'yan takarar gwamnan PDP daga Gombe, Bauchi, Kano, Yobe da Jigawa a gidansa da ke Bamaina.
Tsohon gwamnan ya ce Malam Pantami ya taɓa bayyana PDP a matsayin "jam'iyyar kafirai" a lokutan baya.
Ya ce PDP ta fuskanci suka iri-iri lokacin tana mulki, amma hakan bai sa ya juya mata baya ba.
Ya bayyana cewa bayan zaɓen 2015, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Babatunde Fashola sun kai masa ziyara a Dutse domin su jawo hankalinsa ya shiga APC. Sai dai ya ce ya ƙi amincewa.
A cewarsa, PDP ce ta ba shi damar zama Ministan Harkokin Wajen Najeriya tare da zaɓarsa gwamnan Jigawa har sau biyu. Saboda haka, ya ce ba zai iya watsi da jam'iyyar ba, maimakon haka ya nemi su koma PDP.
Lamido ya kuma yi zargin cewa lokacin da Pantami yake Babban Limamin Masallacin Juma'a na Jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa, ya riƙa wa'azi yana kiran PDP da "jam'iyyar kafirai" tare da yin addu'ar Allah ya kawo ƙarshenta.
Ya ƙara da cewa daga baya Pantami ya shiga PDP bayan bai samu tikitin takarar gwamnan Gombe a APC ba.
Har ila yau, ya ce wannan mataki ya haifar da muhawara da martani daga mutane a kafafen sada zumunta.
Kalaman Lamido na zuwa ne a daidai lokacin da sauya sheƙar 'yan siyasa da shirye-shiryen babban zaɓen 2027 ke ci gaba da ɗaukar hankalin jama'a a faɗin Najeriya.
Wani mai amfani da kafofin sadarwa a Najeriya, Sulaiman Uwaisu Idris ya wallafa guntun bidiyon daidai inda Sule Lamido ke magana kan sukar PDP da Pantami ya yi a shafinsa na X.
An kai karar Pantami kotu kan takara
Mun ba ku labarin cewa Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Gombe ta fara sauraron ƙarar da Khamisu Mailantarki ya shigar kan takarar.
Farfesa Isa Pantami Mailantarki ya yi zargin cewa Sheikh Pantami bai shiga zaɓen fitar da gwani ko sayen fom ba kafin samun tikitin takarar gwamna na PDP.
Kotu ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 9 ga watan Yulin 2026 domin bai wa kowane bangare damar kare kansa.
Asali: Legit.ng

