Abba Kabir da Gwamnonin APC da Ke Neman Tazarce Sun Fadi Matsayarsu kan Tinubu
- Gwamnonin jam'iyyar APC 21 da ke neman tazarce a Najeriya sun yi muhimmiar ganawa a jihar Kebbi
- Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya ce gwamnoni sun amince su yi aiki domin tabbatar da nasarar Tinubu a zaɓen 2027
- Masu fashin baki kan lamuran siyasa a Najeriya na ganin wannan ganawa na daga cikin shirin taimakawa Tinubu a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kebbi - Gwamnonin APC guda 21 sun yi wata muhimmiyar ganawa a jihar Kebbi yayin da ake shirye-shiryen zaben shekarar 2027.
Gwamnonin sun bayyana cewa gyare-gyaren da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa suna da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da ceto tattalin arzikinta.

Source: Twitter
Gwamnonin APC sun gana a Kebbi
Gwamnonin sun bayyana hakan bayan taronsu da aka gudanar a Birnin Kebbi, inda suka sake jaddada goyon bayansu ga manufofin gwamnatin Tinubu, suna cewa ƙasar na gyara kura-kuran da aka tara tsawon shekaru, cewar The Nation.

Kara karanta wannan
Gwamnoni 18 da ke neman tazarce a zaben 2027 sun yi ganawar sirri a Kebbi, an samu bayani
Gwamna Nasir Idris, wanda ya karanta sanarwar taron, ya ce gwamnoni sun amince su yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Ya bayyana cewa goyon bayan nasu ba siyasa kawai ba ne, sai dai saboda sun yi imanin Najeriya na buƙatar shugabanci mai ƙarfin hali, ci gaba da manufofi masu amfani da haɗin gwiwa.
Gwamna Idris ya tura bukata ga yan Najeriya
Idris ya buƙaci 'yan Najeriya su yi haƙuri da ƙalubalen da ake fuskanta a halin yanzu, su duba amfanin da gyare-gyaren za su haifar a nan gaba.
Ya kuma ce gwamnoni sun yi Allah wadai da sace mutane, hare-hare kan makarantu, ta'addanci, garkuwa da mutane da sauran laifukan da ke barazana ga zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Source: Facebook
Alwashin da gwamnonin suka sha a Najeriya
A cewarsa, gwamnoni sun ƙara ƙudirin haɗa kai tsakanin gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da shugabannin al'umma domin kare makarantu da al'ummomi.
Sun kuma nuna damuwa kan rahotannin hare-hare da kashe-kashen da ake zargin ana kai wa 'yan Najeriya da sauran 'yan Afirka a Afirka ta Kudu, tare da neman a gudanar da bincike cikin gaskiya.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun shiga uku, Tinubu ya shirya amfani da fasahohin zamani a Najeriya
A Abuja kuwa, Darakta Janar na Tinubu Support Organisation, Aminu Suleiman, ya ce yankin Arewa zai mara wa Shugaba Tinubu baya, yana mai cewa adalci ya kamata ya ba shi damar kammala wa'adinsa biyu.
Suleiman ya ce bayan Arewa ta yi mulki na tsawon shekara takwas a ƙarƙashin Muhammadu Buhari, ya dace yanzu a bar Kudu ta kammala nata wa'adin domin tabbatar da daidaito, cewar Daily Post.
Tsohon dan takarar PDP ya koma APC
Mun ba ku labarin cewa dan takarar gwamna ƙarƙashin jam'iyyar PDP a Sokoto ya fice daga cikinta zuwa APC mai mulki a jihar.
Dan siyasar ya danganta matakin da jagorancin Sanata Aliyu Wamakko da ayyukan Gwamna Ahmed Aliyu ke yi inda ya yaba masa kan ayyukan alheri.
An karɓi tsohon ɗan takarar gwamna a gidan Wamakko da ke Abuja, inda APC ta ce sauyin ya nuna jam'iyyar na ƙara samun karɓuwa a Sokoto.
Asali: Legit.ng