Yanzun nan Rigima Ta Barke a Majalisar Wakilai kan Bukatar a Gayyaci Tinubu
- An hargitse a zaman majalisar wakilai da aka gabatar da bukatar a gayyaci Shugaba Bola Tinubu ya yi bayani kan jinkirin aiwatar da kasafin 2025
- Benedict Etanabene ya fara cewa sabon umarnin da Akanta Janar ya fitar zai iya kawo cikas ga aiwatar da ayyukan mazabu da kasafin kudin bana
- Kudurin da aka gabatar na gayyatar shugaban kasa ya haifar da cacar baki tsakanin 'yan majalisar yayin zaman da aka gudanar yau ranar Laraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - An samu rikici a zaman majalisar wakilai a ranar Laraba bayan 'yan majalisar sun samu sabani kan wani kudiri da ke neman a gayyaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
An rahoto cewa kudirin da ya jawo ce-ce-ku-cen ya bukaci a gayyaci Tinubu domin ya yi bayani kan jinkirin aiwatar da kasafin kudin shekarar 2025.

Kara karanta wannan
'Abin da Tinubu ya kamata ya yi wa Gbajabiamila kafin binciken ICPC': Hadimin Atiku

Source: Twitter
Zaman majalisar wakilai na ranar Laraba
Lamarin ya faru ne bayan dan majalisa mai wakiltar mazabar Okpe/Sapele/Uvwie ta jihar Delta, Benedict Etanabene, ya gabatar da batu na gaggawa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Etanabene ya ja hankalin majalisar kan wata takarda da Akanta Janar na Tarayya, Shamseldeen Ogunjimi, ya fitar ranar 29 ga Yuni.
A cikin takardar, an umurci dukkan ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya da su dakatar da biyan kudaden ayyukan mazabu da na shiyyoyi (ZIPs), sai dai idan ma'aikatar harkoki na musamman da hulda tsakanin gwamnatoci ta tantance su.
Etanabene ya ce wannan mataki zai kara kawo cikas ga aiwatar da kasafin kudin 2025, yana mai tunatar da cewa majalisar ta taba gayyatar Akanta Janar da wasu ministoci kan matsalar aiwatar da kasafin, amma ba a samu wani gagarumin sauyi ba.
Ya ce 'yan majalisa sun kasa bayyana wa al'ummarsu dalilin da ya sa ayyukan da aka amince da su a kasafin kudi ba su fara ba.
A cewarsa, Najeriya na aiwatar da kasafin kudin shekarun 2024, 2025 da ma 2026 a lokaci guda, lamarin da ya ce bai dace ba, a cewar rahoton Punch.
Rikici ya barke kan 'gayyatar Tinubu'
Saboda haka ya bukaci a gayyaci Shugaba Tinubu cikin gaggawa domin ya yi wa majalisar bayani kan dalilin fitar da wannan umarni da kuma jinkirin aiwatar da kasafin kudin bana.
Bukatar ta raba kan 'yan majalisar, inda da dama suka goyi bayanta, yayin da wasu suka nuna adawa, abin da ya haddasa cacar baki da hargitsi a zauren majalisar.
Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya dauki lokaci kafin ya kwantar da hankulan 'yan majalisar, yana mai bayyana cewa batutuwan da aka gabatar karkashin batu na gaggawa ba sa bukatar muhawara.

Source: Facebook
An sake kaurewa kan wata bukatar
Daga bisani, dan majalisa mai wakiltar Aba ta Arewa da Kudu a jihar Abia, Alex Mascot, ya gabatar da wani kudiri na gaggawa, yana mai cewa ya kamata a gayyaci Shugaba Tinubu ya yi bayani kan yadda ake aiwatar da kasafin, musamman ganin biliyoyin nairori da gwamnati ke warewa bangaren tsaro.

Kara karanta wannan
Tinubu ya waiwayi manyan kamfanonin kafafen sadarwa, za a binciki Meta, X da sauransu
Sai dai shugaban kwamitin kula da rundunar ruwa na majalisar, Yusuf Gagdi, ya yi adawa da kudirin, yana mai cewa ya fi dacewa a gayyaci jami'an da ke da alhakin aiwatar da kasafin maimakon shugaban kasa.
Hakan ya jawo wasu 'yan majalisa suka katse shi suna bukatarsa ya zauna.
Yadda majalisa ta amince da kasafin 2025
Tun da fari, mun ruwaito cewa, majalisar wakilai ta amince da kasafin 2025 na Naira tiriliyan 54.99 domin raya ƙasa, biyan basussuka da inganta tattalin arziki.
An ware Naira tiriliyan 23.963 domin manyan ayyuka, yayin da aka ware Naira tiriliyan 14.317 don biyan basussuka da nauyin kuɗi.
Shugaba Bola Tinubu ya ce an samu ƙarin kuɗin shiga a FIRS, Kwastam da hukumomi, wanda ya sa kasafin ya kai N54.99trn.
Asali: Legit.ng
