Tsohon Minista Ya Tona Asirin ‘Yan Majalisar da Suka Nemi Cin Hancin N200m

Tsohon Minista Ya Tona Asirin ‘Yan Majalisar da Suka Nemi Cin Hancin N200m

  • Solomon Dalung ya zargi ‘yan majalisa da neman ya biya cin hanci wajensa a shekarun da yake minista a gwamnati
  • ‘Dan siyasar ya yi shekaru kusan hudu a matsayin ministan matasa da wasanni a mulkin Muhammadu Buhari
  • Domin majalisa ta amince da kasafin kudinsu, Dalung ya ce wasu abokan aikinsa sun rika biyan cin hancin kudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Tsohon ministan harkokin matasa da wasanni, Solomon Dalung ya yi zargin cewa ‘yan majalisa sun nemi cin hanci daga wajen shi.

Barista Solomon Dalung ya ce ‘yan majalisar Najeriyan sun bukaci ya biya cin hanci na N200m lokacin da ya nemi kare kasafin kudin ma’aikatarsa.

Solomon Dalung
Ministan matasa da wasanni a 2015, Solomon Dalung da 'Yan majalisar tarayya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Solomon Dalung ya zargi majalisa da cin hanci

A ranar Laraba ne jaridar Daily Trust ta rahoto tsohon ministan yana wannan bayani a wani jawabi da ya fitar yana tuna lokacin da yake ofis.

Kara karanta wannan

Mubarak Mnisi: Yadda dan babban fasto ya bar Kiristanci zuwa Musulunci

Solomon Dalung wanda ya yi minista a mulkin marigayi shugaba Muhammadu Buhari ya nuna yadda rashin gaskiya ta yi kane-kane a Najeriya.

Dalung ya shaida cewa an gabatar masu da wannan bukata ne jim kadan bayan ya je gaban ‘yan majalisar tarayya ya kare kasafin kudin shi.

Jim kadan bayan an yi hakan, ‘yan majalisar suka nemi ya biya N200m, cin hancin da bai da alaka da amincewa da kudin da ma’aikatarsa za ta kashe.

"Na duba takardar kasafin kudin da yake gaba na, na fada masu ban ga bangaren da aka rubuta ‘cin hanci’ ba.
Na fada wa kwamitin cewa tunda babu wannan bangare a kasain kudin ma’aikatar, ban san ina ku ke so in samo N200m ba."

- Solomon Dalung

'Yan majalisar sun hakura sun rabu da minista

Tsohon ministan ya ce da wannan magana ne ya rufe bakin ‘yan kwamitin majalisar tarayyar.

Sai kawai suka ce mani, ‘Shikenan minista, mun yi maka uzuri. Za mu dangana da Babban sakatare’

Mista Dalung wanda shi kan shi lauya ne ya ce rawar da yake taka wa wajen kare kasafin kudi ya ragu sosai bayan wannan takaddama.

Kara karanta wannan

Yadda shugaban ma'aikatar bogi ya yaudari mataimakin shugaban majalisar wakilai

A cewarsa da zarar ya gabatar da kasafin kudinsa na shekara, ‘yan majalisa sukan ce ya yi tafiyarsa, sai a zauna da manyan jami’an ma’aikatarsa.

Ya ce daga baya ya gano cewa ba ma’aikatar matasa da wasanni kurum abin ya shafa ba, dole wasu ministoci suka rika biye wa ‘yan majalisar.

Solomon Dalung
Tsohon minista Solomon Dalung da wani abokin aikinsaa gwamnatin Muhammadu Buhari Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wasu ministoci sun rika ba majalisa cin hanci

Domin ganin an yi na’am da kasafin kudinsu, ya ce wasu ministoci har na kusa da Muhammadu Buhari sun rika bada cin hancin miliyoyi.

A jawabinsa, babban 'dan siyasar bai kama sunayen wadanda suka bada ko suka karbi hancin ba. Labarin nan ya bayyana a tashar Trust Radio.

Zuwa yanzu majalisa ba ta tanka 'dan adawan ba, kuma shi ma bai kawo wasu hujjoji da za su tabbatar da wannan zargi mai nauyi da ya yi ba.

Tsohon minista zai yi shari'a da hukumar ICPC

An ji labari kashin tsohon ministan Bola Tinubu zai bushe, lauyan EFCC ya shigar da karar shi a kotu saboda wasu zargi shida da ake yi masa

Kara karanta wannan

Peter Obi ya sake bukatar Tinubu ya yi murabus kan badakalar da IMF ta tono

Za gurfanar da tsohon ministan kimiyya da fasaha, Chief Uche Geoffrey Nnaji saboda samun shi da amfani da takardun bogi, zargin da ya karyata.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta shigar da zarge-zargen laifuffuka gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a kan Uche Nnaji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng