Bayan Hukuncin Kotu, NDC Ta Bayyana Makomar Takarar Peter Obi da Kwankwaso a Zaben 2027
- Jam'iyyar NDC ta yi fatali da hukuncin babbar kotun tarayya mai zama a Lakoja, wanda ya rusa rijistar da aka mata a matsayin jam'iyyar siyasa
- NDC ta tabbatar wa Peter Obi, Kwankwaso da sauran 'yan takararta cewa hukuncin ba zai hana jam'iyyar shiga babban zaben 2027 ba
- A sanarwar da ta fitar yau Juma'a, jam’iyyar NDC ta ce ta umarci lauyoyinta su garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar hukuncin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam’iyyar NDC ta tabbatar wa ‘yan takararta na zaɓen 2027 cewa hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta yanke ba zai hana ta shiga babban zaɓe mai zuwa ba.
Wannan na zuwa ne bayan kotun ta soke wani tsohon hukunci da ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi wa NDC rajista a matsayin jam’iyyar siyasa.

Source: Twitter
Daily Trust ta kawo cewa kotun ta ce hukuncin da aka yanke a ranar 10 ga Disamban 2025 yana da nakasu a tsarin doka domin an yanke shi ba tare da sauraron dukkan ɓangarorin da abin ya shafa ba.
NDC ba ta gamsu da hukuncin kotun ba
A wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Moses Cleopas Zuwoghe, ya sanya wa hannu ranar Juma'a, NDC ta bayyana rashin gamsuwarta da hukuncin da aka yanke.
Jam’iyyar ta bayyana cewa tun a watan Disamban 2025 ta samu hukuncin kotu da ya tilasta wa INEC yi mata rajista bayan hukumar ta ƙi amincewa da buƙatarta.
NDC ta ƙara da cewa tun bayan rajistar da aka yi mata a ranar 5 ga Fabrairun 2026, ta gudanar da ayyuka a faɗin ƙasar nan, ciki har da rajistar mambobi, zaɓukan shugabanni daga matakin mazaba zuwa na ƙasa.

Kara karanta wannan
Rajistar NDC: Takarar Obi da Kwankwaso ta gamu da koma baya da kotu ta yanke hukunci
Jam’iyyar ta bayyana cewa ta shiga zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a jihohin Nasarawa da Enugu, sannan ta riga ta tsayar da ‘yan takara da za su shiga zaben 2027.

Source: Facebook
Idan ba ku manta ba NDC ta tsayar da Peter Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa d Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin mataimakinsa.
Sanarwar ta ce:
“Ƙungiyar da ta shigar da ƙara a kotu ba jam’iyya ce mai rajista ba. PMP ta yi iƙirarin cewa tun 2015 ta nemi rajista amma aka ƙi amincewa da ita.”
Jam'iyyar NDC za ta ɗaukaka ƙara
Jam’iyyar NDC ta ce ta umarci lauyoyinta su garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar hukuncin, kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.
Ta kuma tabbatar wa mambobinta da ‘yan takararta cewa dukkan ayyukan siyasar da ta gudanar suna nan daram.
NDC ta kawo sabon tsari kafin 2027

Kara karanta wannan
A wata 1 kacal, hukumar kwastam ta tara kudin shiga sama da Naira biliyan 100 a tashar TinCan
A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar NDC ta umurci dukkan ’yan takarar da ta tsaida su sanya hannu kan takardar rantsuwa kafin a mika sunayensu ga hukumar INEC.
NDC ta ce manufar wannan mataki ita ce kare kuri’un jama’a, karfafa da’a a cikin jam’iyya da kuma dakile yawaitar sauya sheka bayan an ci zabe.
Dokar ta shafi ’yan takarar gwamna, majalisun dokokin tarayya da na jihohi, amma ba ta hau kan 'dan takarar shugaban kasa, Peter Obi da mataimakinsa, Rabiu Kwankwaso ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
