'Yan Ta'adda na Barazana a Iyakokin Najeriya, Sojoji Sun Shirya Murkushe Su
- Rundunar sojin Najeriya ta ce ta gano alamun ‘yan ta’addan ƙasashen ketare na barazana a kan iyakokin kasar nan, kuma ta shirya murƙushe su
- Hafsun sojin kasa ya ce sama da kashi 80% na sojojin Najeriya na gudanar da ayyukan yaƙi da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuffuka
- Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zamanantar da rundunar soji ta hanyar amfani da fasahohin zamani da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana a ranar Litinin cewa rundunar sojin Najeriya ta gano alamun ‘yan ta’adda daga ƙasashen waje a kan iyakokin Najeriya.
Laftanar Janar Waidi Shaibu ya tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa rundunar za ta ɗauki matakin da ya dace domin murƙushe barazanar.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun shiga uku, Tinubu ya shirya amfani da fasahohin zamani a Najeriya

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa ya bayyana hakan ne a wajen bikin rufe Ranar Sojojin Najeriya ta 2026 da aka gudanar a Port Harcourt, Jihar Rivers, wanda Shugaba Bola Tinubu ya samu wakilcin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Barazanar 'yan ta'adda a iyakoki
Najeriya ta yi magana kan barazanar 'yan ta'adda a iyakoki ne bayan a baya-bayan nan an samu hare-haren ‘yan ta’adda a ƙasashen maƙwabta, ciki har da harin da JNIM ta kai filin jirgin sama a kasar Nijar.
Haka kuma, ƙungiyar ISWAP ta yi ƙoƙarin kutsawa tare da ƙwace sansanonin sojoji a Najeriya, amma dakarun soji sun samu nasarar dakile hare-haren.
Da yake jawabi, the Cable ta rahoto Waidi Shaibu ya ce:
“Mun riga mun gano alamun motsin ‘yan ta’addan ƙasashen waje a kan iyakokinmu. Ina tabbatar wa kowa cewa rundunar sojin Najeriya a shirye take kuma za ta iya tunkarar wannan barazana.”
Ya ƙara da cewa kamar yadda tsofaffin sojojin Najeriya suka yi nasara a yaƙe-yaƙen duniya na farko da na biyu, yaƙin basasar Najeriya da kuma ayyukan ECOMOG, haka ma sojojin wannan zamani za su yi nasara.

Source: Facebook
Najeriya za ta sabunta dabaru
Hafsun sojin ya ce rundunar sojin Najeriya na ci gaba da sabunta dabarunta bisa sauye-sauyen yanayin tsaro, tare da ci gaba da kare ‘yancin kai da cikakken ikon ƙasar.
Laftanar Janar Waidi Shaibu ya bayyana cewa rundunar na aiki ne bisa ginshiƙan sadaukarwa, biyayya, mutunci, jaruntaka da ƙwazo.
Ya ce bikin na wannan shekara ya zo ne a daidai lokacin da sama da kashi 80 cikin 100 na sojojin Najeriya ke gudanar da ayyukan tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.
An dauki sojoji 14,000 a Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa hafsun sojin kasan Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shuaibu ya sanar da cewa an dauki dakarun soji 14,000 a fadin kasar nan.
Ya bayyana cewa daukar sojojin na cikin tsarin da shugaban kasa Bola Tinubu ya kawo don daukar dakaru 28,000 domin kara yawan sojoji.
Shugaban sojojin ya kara da cewa an ba dakarun cikakken horo a cibiyoyi uku da ke fadin Najeriya domin cigaba da yaki da 'yan ta'adda a sassan kasar nan.
Asali: Legit.ng
