Zaɓen 2027: Jonathan Ya Wanke Kansa kan Zargin Karɓo N500bn don Raba Kuri'ar Obi
- Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya martani kan rahoton da ke cewa an yi masa tayin Naira biliyan 500 domin ya tsaya takara
- Mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai ya ne ya yi martani a madadinsa bayan an fara raɗe-raɗin ya karɓo kwangilar raba ƙuri'ar Peter Obi
- Raɗe-raɗin na kara yin karfi ne bayan rahotanni na ci gaba da cin karo da juna a kan zai tsaya wa tsagin PDP takarar shugaban ƙasa a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja – Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi watsi da wani rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa an yi masa tayin Naira biliyan 500 domin ya tsaya takarar shugaban kasa.
Rahoton ya kara da zargin cewa ya karbi kudin domin ya yi hamayya da ɗan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi, domin raba ƙuri'un yankin Kudu maso Kudu.

Source: Getty Images
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa Mai ba Jonathan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dakta Ikechukwu Eze, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi5 ga watan Yuli, 2026 a Abuja.
Jonathan ya musanta zargi kan takarar 2027
A ruwayar Leadership, Dakta Ikechukwu Eze ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya tsagwaronta, marar tushe kuma wanda aka kirkira domin ya jefa tsohon shugaban kasar cikin cece-kuce na siyasa.
Ya bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da labarin, yana mai cewa wani ƙaramin shafin intanet ne ya wallafa shi tare da jingina wa Jonathan kalaman da bai taba furtawa ba.
A cewarsa, rahoton bai cika ko mafi ƙarancin ƙa'idojin aikin jarida ba, domin bai bayyana inda ko yaushe Jonathan ya yi irin wannan magana ba, ko kuma wanda ya yi masa tayin kudin.
Jonathan ya yi gargaɗi kan yaɗa karya
Dakta Eze ya ce rahoton bai ambaci mutanen da suka halarci wurin da ake zargin an yi wannan tayi ba, haka kuma bai bayyana wanda ya yi tayin kudin ba.

Kara karanta wannan
Mutumin da ya sayar da yaron abokinsa a kan N1.3m ya tona yadda suke satar yara a Najeriya
Ya ce wannan na nuna alamun cewa an ƙirƙiri labarin ne kawai domin ya yaudari jama'a tare da haddasa rikicin siyasa da ba shi da amfani.

Source: Getty Images
Mai ba tsohon shugaban kasan shawara ya kuma bayyana cewa irin waɗannan labaran ƙarya kan karu ne yayin da ake tunkarar lokutan siyasa.
Saboda haka, ya shawarci 'yan Najeriya da su guji yarda da duk wani labari mai dauke da manyan ikirari ba tare da tabbatar da sahihancinsa daga ingantattun kafofin yada labarai ba. Sanarwar ta jaddada cewa Goodluck Jonathan bai taba karɓa ko tattauna wani tayin Naira biliyan 500 da ake ikirarin an yi masa ba, yana mai roƙon jama'a su yi watsi da rahoton gaba ɗaya.
Jonathan ba zai yi takara ba – Majiya
A baya, kun samu labarin cewa makusantan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan sun warware batun shirin da ake yi na tsaida shi takarar shugaban ƙasa zaɓen 2027.
Sun ce babu wata alama da ke nuna Jonathan na neman sake neman takara, tare da zargin cewa wasu na amfani da sunansa domin cimma muradunsu na siyasa.
Sai dai wani ɓangaren PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya dage cewa Jonathan ne ɗan takararsu na shugaban ƙasa a 2027 tare da bayyana dalilinsa.l
Asali: Legit.ng
