Dan Takarar Sanata Ya Yi Wa APC Gardama kan Batun Sauya Sunan Shi

Dan Takarar Sanata Ya Yi Wa APC Gardama kan Batun Sauya Sunan Shi

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sauya sunayen wasu 'yan takara da suka samu nasara a zaben fitar da gwanin da ta gudanar
  • Dan takarar kujerar sanatan Taraba ta Arewa, Hon. Kabiru Bello Badawaire, ya fito ya yi magana kan batun cewa an sauya sunansa da na sanata mai ci
  • Kabiru Bello Badawaire ya musanta cewa ya janye daga takarar, inda ya tunatar da APC kan ta bi ka'ida yadda ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Taraba - Dan takarar Sanata na yankin Taraba ta Arewa karkashin jam'iyyar APC, Hon. Kabiru Bello Badawaire, ya yi magana kan batun janye takara.

Kabiru Bello Badawaire ya bayyana cewa ba zai janye wa kowane mutum da ke takara a wannan kujerar ba.

Badawaire ya ce ba zai janye daga takara ba
Kabiru Bello Badawaire da shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: Hon. Kabiru Bello Badawaire, Senator Uba Sani
Source: Facebook

Dan takarar na APC ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 4 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

"Ka da ku bata kuri'unku"; Sanata Kalu ya bayyana abokin hamayyar Tinubu a 2027

Haka kuma, Hon. Badawaire ya bayyana cewa an zabe shi kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tabbatar da shi, kuma yana nan a matsayin dan takarar jam'iyyar APC na wannan kujera.

Me Kabiru ya ce kan janye takara?

Ya karyata ikirarin da ke yawo a kafafen yada labarai na cewa jam’iyyar ta sauya sunansa da na mai ci a yanzu, Sanata Shuaibu Isa Lau, a matsayin dan takarar jam’iyyar na wannan kujera.

“Ba zan janye daga takarar sanata mai wakiltar yankin Taraba ta Arewa ba. Ni ne dan takara, kuma ba zan janye wa kowane mutum ba."
“Ba zan iya sayar da hurumin da talakawa suka ba ni ba. Ban san da batun sauya ni ba, kuma jam’iyyar ba ta tuntube ni ba."

- Hon. Kabiru Bello Badawaire

Ya tunatar da jam'iyyar APC

Dan takarar sanatan na yankin Arewa na jihar Taraba ya bayyana cewa sashe na 29 na dokar zabe ya bayyana karara cewa lallai sai dan takarar da aka zaba da kansa ya yanke shawarar janyewa daga takara kafin jam'iyyar ta iya musanya shi da wani dan takarar.

Kara karanta wannan

2027: Malami ya gana da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a Abuja

“Ba na kama da wanda zai janye daga takarar, kuma wannan shi ne matsayina. Dole ne jam’iyyar ta mutunta bin ka'ida."
“Ikirarin cewa an sauya ni ba tsarin dimokuradiyya ba ne. Ana iya sauya dan takara ne kawai idan an sanar da shi yadda ya kamata kuma ya amince da hakan, ko kuma idan ya rubuta wa jam’iyyar da radin kansa game da shawararsa ta janyewa daga takarar."
“Ina so na sanar da mutanen Taraba cewa ba a sauya sunana da na kowane mutum ba. Ina nan a matsayin dan takarar sanata na jam'iyyar na yankin Taraba ta Arewa, kuma ba zan janyewa kowa ba."

- Hon Kabiru Bello Badawaire

Badawaire ya musanta janyewa daga takara
Dan Takarar Sanatan APC a Taraba ta Arewa, Kabiru Bello Badawaire Hoto: Hon. Kabiru Bello Badawaire
Source: Facebook

Dalilin APC na sauya 'yan takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta dauki matakin sauya sunayen wasu 'yan takara na sanatoci da 'yan majalisar wakilai.

APC dai ta cire wasu 'yan takarar sanata guda shida da 'yan takarar majalisar wakilai guda 19, wadanda suka yi nasara a zaben fitar da gwani.

Shirin mayar da ikon jam'iyyar a jihohi ga gwamnoni da manyan masu ruwa da tsaki shi ne ya janyo aka ajiye wasu daga cikin 'yan takarar a gefe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng